Rusau a Kano: Ƙungiya ta yi barazanar maka Gwamna Abba a kotu

  • Ta bai wa Gwamnan sa’o’i 72 ya janye aikin rusau da yake yi

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Good Governance and Change Initiative (GGCI), ta bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, wa’adin sa’o’i 72 a kan ya dakatar da rusau da yake yi a jihar sannan ya gayyato ‘yan kasuwa da ɗaiɗaikun mutanen da lamarin ya shafa don warware matsalar cikin ruwan sanyi.

Ƙungiyar ta yi barazanar maka Gwamnan a kotu muddin wa’adin da ta shata masa ya ƙare ba tare da yin abin da ya kamace shi ba.

Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata a Abuja, babban jami’in ƙungiyar na ƙasa, Okpokwu Ogenyi, ya bayyana takaicinsa kan salon shugabancin Gwamnatin Kano mai ci ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP.

Tare da nuna mamakin yadda a makon da gwamnatin ta kama aiki, a makon ne kuma ta fara rushe gine-ginen jama’a ba tare da nazarin bayanan da gwamnatin da ta gabace ta ta miƙa mata ba.

A cewar Ogenyi, Gwamna Abba Yusuf ya ba da umarnin rushe filaza mai ɗauke da shaguna 90 da Daula Hotel wanda darajarsa ta kai sama da Naira biliyan 10 da dai sauransu.

Ogenyi ya kuma bayyana rusau da Gwamna Abba ke yi a matsayin rashin mutunci wanda ya yi sanadiyar raba dubban mutane da matsugunansu ba tare da gwamnati ta damu da halin da ta jefa su ciki ba

A cewar ƙungiyar, “Mun lura sosai da irin ɓarnar da aka tafka a garin Kano wanda ya haɗa da asarar rayuka sama da ashirin na ‘yan Nijeriya da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar.

“Gwamnati ta yi iƙirarin mutum biyu ne suka mutu, amma tawagarmu da ta ziyarci Kano ta ce sama da mutum 20 ne suka mutu wanda hakan kuwa babban abin damuwa ne.”

Ƙungiyar ta ƙara da cewa, “Muna kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta shiga tsakani sannan ya ja hankalin Gwamna Abba Yusuf a kan ya dakatar da ci gaba da rusau da yake yi ba bisa ƙa’ida ba wanda ke haifar da asarar rayuka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *