Daga MUSBAHU BAFFA
A Gwamnatance komai na tafiya ne da tsari bisa doron mu’amala da al’ummar da ake mulka. Yayin da duk aka rasa hakan tsakanin Gwabnati da al’umma, tabbas ba mulkarsu ake ba, bautar da su ake.
Mai girma Gwabna, mun san cewa ana rushe gini domin sabuntawa ko kuma don kwaskwarima ko kuma sake fasali yayin da duk buƙatar hakan ta taso. Sai dai yana da kyau a fahimtar da al’ummar gari don su fahimta, domin suna da haƙƙin hakan.
Mai girma Gwabna, tsohon Gwabnan Kaduna da ya gabata ya rushe gadar Kawo, inda ya sabuntata. Kuma tabbas sabuntawar ta fi wacce aka rushe amfanar da jama’a. Amma fa ba kawai wayar gari aka yi aka ga ana rushe ta ba, sai da ya yi wa al’ummar da yake mulka bayanin dalilin rushewar.
Mai girma Gwabna, ko da rushe wannan shatalelen na da amfani tabbas ba a rushe shi a kan lokacin da ya dace ba. Ba a kuma rushe shi ta salon da ya dace ba.
Mai girma Gwabna, kamata ya yi a fahimtar da al’umma dalilin da ya sa za a rushe kafin su ga ana rushewar. Ko ba komai hakan ya isa shaida da kuma nuna cewa domin amfanin al’ummar aka rushe.
Mai girma Gwabna, a wannan gavar da Gwabnatinka ke ta rushe-rushe, zai matuƙar wahala al’umma su aminta da duk wata hujja da za ka bayar, ko ‘yan koronka za su bayar kan dalilin rushe wannan shatalelen.
Domin kuwa, kafin rusawa ya dace a faɗi dalilan, ta yadda al’umma ba za su gwama dalilin rushewar da sauran dalilan da ya sa Gwabnatinka ke rusau ba.
Mai girma Gwabna, kuskure ne rushe wannan shatalelen cikin dare matuƙar dalilin rushewar da ake bayarwa shi ne dalili a wajenka.
Domin kuwa salon ya yi dai-dai da irin salon rusau ɗin da Gwabnatinka ke yi a halin yanzu. Bisa wannan salon kaɗai ba lallai al’umma su fahimci dalilin da ake fitarwa ɗin ba.
Mai girma Gwabna, yana da kyau ka tsaya ka yi kyakkyawan tsari wajen mu’amalar sadarwa tsakaninka da al’ummar Jahar Kano, domin tabbas akwai ƙwaƙwƙwarar rashin fahimta tsakaninka da su.
Mai girma Gwabna, wannan shi ne saƙona na biyu gare ka a matsayinka na Gwabna. Kuma insha’Allahu, duk lokacin da na ga dacewar rubuto irin wannan saƙon zan rubuta, ko na rubuto kai tsaye zuwa gare ka.
Saƙo daga Musbahu Baffa (Na Ƴar Talla). Masoyin Jahar Kano, kuma Bakwankwashe.