Ruwan jiki (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu, assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilimintu, kuma ku san yadda jikinku ke aiki.

Bayani ya zo a satin da ya gabata game da ruwan jikin ɗan Adam. Na faɗi guraren da ake samun ruwan jiki, da gwargwadon yawan ruwan jiki da ake samu a jikin ɗan Adam. Na faɗa cewa akwai ruwa a cikin ƙwayoyin halitta, wato kowacce ƙwayar halitta ta jikin ɗan Adam. Amma zanyi ƙarin bayani domin a ƙara ganewa. Akwai ruwa tsokar nama, akwai ruwa cikin jini, akwai ruwa a cikin ƙashi, akwai a cikin fatar da ta lulluɓe jikinmu.

Malam Bahaushe ya na cewa: “ruwa abokin aiki”. A cikin jikin ɗan Adam ma, haka abin ya ke. Mafi yawan sashen jikin ɗan Adam duk ruwa ne. Amma idan na ce ruwa ba ina nufin ruwa da muka Saba gani ba; shi wannan ruwa ne na musamman mai ɗauke da narkakkun sinadarai kala-kala waɗanda ke tabbatar da daidaituwar ayyukan jikin bil adama.

Abinda na manta ban faɗa ba satin da ya gabata shi cewa akwai ruwan a cikin shi kansa idon ɗan Adam. Kwatancen da zanyi don a gane shi ne: Iowa ya San akwai ruwa a cikin tumatiri. Wannan ruwa shi yasa tumatirin yayi vul-vul. Shi ma ido haka yake.

Akwai kuma wani ruwa a cikin tumbin ɗan Adam mai matuƙar zafi. Abinda nature ke cewa “acid” to shi na ke nufi. Wannan ruwa yana taimakawa wajen narka abinci yayin da ya shiga tumbi, kuma ya na farkar da sauran sinadarai da su zama ciki shiri wajen narka sauran sashen abincin.

Bayan haka, akwai kuma ruwan da ke kewaye da gavvai a inda yake taimakawa wajen bayar da kariya ko rage gugar juma saboda matsuwa (misali kayan cikin ɗan Adam kewaye su ke da wani tsinkakken ruwa). Akwai ruwa a cikin ƙoƙon kai Wanda ƙwaƙwalwar mutum ke wanka a ciki. Kamar dai yadda za ka sanya abu mai ɗan nauyi akan ruwa ya dinga yawo ba tare da ya nutse ba, to haka itama ƙwaƙwalwa take nunƙaya a cikin wannan ruwa. Sai dai ita ƙwaƙwalwa a Katange ta ke cikin ƙoƙon kai. Saboda haka ta na da iyaka wajen kai-kawo, wato daga ɓangaren hagu zuwa na dama. A cikin wannan ruwa akwai sinadaran da ke bawa ƙwaƙwalwa abinci. 

Halittun da ke cikin kogon ƙirji, musamman huhu, Wanda yake a kewaye da wata da jaka shi ma a kewaye yake da wani ruwa mai santsi da yake bashi dama ya gogi bangwayen kogon ƙirji (daga ciki) ba tare da ya samu wata illa ba. Ita ma zuciya ta ɗan Adam cikin wata jaka ta ke, a cikin jakar akwai wani ɗan ruwa mai santsi da yake hana siɗewar zuciya yayin da take gugar halittun da ke maƙwabtaka da ita.

Kogon da ke ƙugu shi ma haka abin yake. Mafitsara, ƙarshen ‘ya ‘yan hanji, mahaifa, da sauran halittu ba ƙamas su ke ba! Akwai wannan ruwan da ke tabbatar da cewa kullum cikin danshi su ke. Itama laakar da ke bayan mutum, a kewaye take da ruwa. Ruwan da ya kewaye ƙwaƙwalwa Wanda nayi bayaninsa ɗazu shi ne yake zartowa har jikin jakar da laka take.

Kafin na yi duba izuwa muhimmanci na ruwan jiki, ina so in ƙara bayani akan ruwa da jiki ya ke samarwa a lokuta na musamman; Wato lokacinda buƙatar a samar da su ta taso. Wanda zan fara da shi, shi ne hawaye. Akwai kuttun da ke zubo dashi, a geffen hanci dama da hagu, daga sama. Ana zubo shi ne yayin da mutum ya shiga yanayi na tsananin farin ciki ko baƙin ciki, ko lokacinda wani baƙon abu ya shiga ido ko hanci. Akwai kuma ruwan da ake samarwa yayin da sha’awa ta motsa wa ɗan Adam.

Wani zai iya cewa ina matsayin ruwan da ke biyo baya idan ɗan Adam ya ji rauni ko ciwo? Shi wannan ruwa ai daga cikin jini ya ke. Akwai kuma ruwan maniyyi da ake fitar dashi yayin saduwa, duk da cewa shima yana fita yayin da sha’awa ta kai matuqa!. Majina ta ɗan banbanta da sauran saboda kaurinta da kuma sassan da su ke samar da ita. Manyan guraren da ake samar da majina guda biyu ne: hanyar abinci, musamman a cikin uwar hanji ida ake samar da bahaya; sai kuwa hanyar iska, Wato inda mu ke shaƙar numfashi.

Gumi shi ma ruwa ne da ke samar da shi saboda wasu dalilai. Na farko yayin da zafi yayi yawa a cikin jikin ɗan Adam, ruwan gumi Wanda yake da ɗumi ya na barin jiki saboda zafin ya ragu, daga baya sai jikin yayi sanyi. Na biyu gumi na tsattsafowa yayin da ɗan Adam ya shiga wani yanayi na ni ‘ya su. Na uku kuwa shi ne lokacin da mutum ke motsa jiki.

Yanzu zan ɗan yi bayani kan muhimmancin ruwan jiki a rayuwar can Adam. Kai tsaye idan babu ruwa a jikin ɗan Adam, ni ban ga ta yadda zai iya rayuwa ba! Idan za ku ita tunawa satin da ya wuce, na buga misali da ayar Al-ƙur’ani da ke nuna cewa duk wani abu mai rai daga ruwa yake. Saboda muhimmancinsa, kaso sittin na duk jikin ɗan Adam ruwa ne, kwatankwacin lita 42 kenan. Kamar yadda zan yi bayani nan gaba idan na samu hali, abubuwan da ke kawo tazgaro ga adadin ruwan jikin ɗan Adam na kawo wahalhalu da rashin lafiya ga jiki.

Ruwan jikin ɗan Adam cibiya ce ta musayar sinadarai, saƙonni, da kuma sufurin narkakkun abubuwa irinsu abinci, maguguna, da sinadarai kala-kala. Duk wani abu da zai taɓa ruwan jiki ashe zai taɓa waɗannan abubuwa da lissafa!

Ruwan jikin ɗan Adam ya na taimakawa wajen tabbatar da surar jilin ɗan Adam. Saboda kyakkyawan tsari da zubi da Mahalicci Ya yi wa jikin ɗan Adam, ya tsara wani wajen ya tasa, wani wajen ya loɓa ko ya ranƙwafa, hakan duk yana da alaƙa da yawa, da zubi na ruwan da ke wannan sashe. Kalli dai ruwan da ke kewaye da ƙwaƙwalwar ɗan Adam! Ba dan da shi ba, to da ƙwaƙwalwa ta yi mana nauyi, tafiya ma sai ta gagare mu!

Masu karatu ku tara a sati mai zuwa domin ci gaba da kawo muku bayanai akan jikin ɗan Adam. Kafin nan nake cewa Assalamu alaikum.