Daga BASHIR ISAH
Rahotanni daga ƙasar Chana sun ce, an samu ambaliya mai ƙarfi a wasu sassan ƙasar, musamman a yankunan Mentougou da Fangshan da ke birnin Beijing na kasar, sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a yankunan da lamarin ya shafa.
An ce ambaliyar ta yi sanadiyyar lalata matsugunnan al’ummar yankin da dama, ta kuma haifar da zaizayar ƙasa.

Ɗan jarida daga ƙasar, Murtala Zhang, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba cewa, “…mamakon ruwan sama da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi, wanda ba a taɓa ganin irin ƙarfinsa ba a shekaru 140 da suka gabata, ya haifar da bala’in ambaliyar ruwan tare da zaizayar ƙasa a wasu yankunan Beijing.

“Inda ma’aikatan ceto ke himmatuwa wajen sake tsugunar da mutane tare da kai musu ɗauki.
“Jama’a don Allah ku ci gaba da yi wa al’ummar ƙasar Sin, musamman Beijing, addu’a da fatan alheri. Allah Ubangiji Ya kiyaye, Ya kare na gaba,” in ji Murtala.
