Ruwan sama ya yi sanadiyar mutuwar mutane 94 a Brazil

Aqalla mutane 94 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da kuma zabtarerwar ƙasa a Brazil bayan an shafe tsawon lokaci ana shatata ruwan sama kamar da bakin-kwarya.

Lamarin ya auku ne a birnin Petropolis mai cike da wuraren ƙayatarwa da yawon buɗe ido kamar yadda hukumomin ƙasar suka bayyana.

Bayanai na cewa, akwai yiwuwar samun ƙarin mamata, ganin yadda alƙalumansu ke ci gaba da ƙaruwa sannu a hankali a daidai lokacin da masu aikin ceto ke ta ƙoƙarin nemo masu sauran numfashi.

Dimbin mutane ne dai ke ci gaba da makalewa a cikin laka da kuma tarin buraguzai.

Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun ɓace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Talatar da ta gabata.

Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.