Ruwan tumfafiya: Tattaki a yanar gizo, leƙe cikin zaurukan ‘Yahoo Groups’

Tattarowa: Khalid Musa

Hausawa su ka ce kishi kumallon mata. Duk da cewa ba mata ne kawai su ka kaɗaita da halittar kishi ba, mazaje ma a nan ba su tsira ba amma ya fi shahara ga mata domin karancin juriyarsu gare shi. Wannan muhawara ta Ruwan Tumfafiya an yi ta ne a kan Kishi ko Kishiya.

Wata Marubuciya Salamatu Adamu ita ce ta haifar da wannan muhimmiyar Muhawar a dandalin Marubuta na Yahoo wacce ta samu gudunmawar wasu hazikan Marubuta da su ka ja zaren muhawar abinda ya kara ma ta armashi. Wadannan Marubuta sune: Habibiy, Muhammad Fatuhu Mustapha da Nasiru Yaro. Kafin mu tsunduma cikin nazarin Muhawarar bari mu fara da tambayar kan mu wai shin menene kishi a mahangar malaman sanin zuciya da kallafe-kallafenta wadanda a ke kira Malaman Ma’arifa. Shaihin Malami Ibnul Kaimi al-Jauziyyah ya kasafta kishi ya zuwa gida biyu, sune:

  1. Kishi don wanda ake so,
  2. Kishi a kan wanda a ke so

Na farko, wato kishi domin wanda a ke so shi ne bai wa masoyi kariya yayinda wani ya nemi wulakanta shi ko ya keta alfarmar mutumcinsa ya cutar da shi. Ya kan yi fushi ya nuna damuwarsa domin an taba zuciyar masoyinsa da wani abu da ya cutar da shi. Irin wannan kishi ya kan angiza masoyi ga yin gaggawar kai ɗauki ga abin kaunarsa ta hanyar sadaukar da ransa da dukiyarsa domin ba shi kariya ga barin cutarwar makiya ko abokan gaba.

Amma nau’i na biyu wato kishi a kan wanda a ke so shi ne kiyayyar yin taraiya da wani ko wata cikin zuciyar mai so ko wanda a ke so. Kishi abu ne mai kyau amma ya kan munana har a kira shi mummuna. Sannu a hankali nazarin wannan muhawara zai nusar da mu nau’ikan kishi tare da faiyace kyawunsa gami da muninsa nan gaba kaɗan ba da dadewa ba.

Da farko dai marubuciyar ta bude wannan muhawarar ne da baituka 38 waɗanda suke nasiha ce ga mata da su bar baƙin kishi duk da ta nuna bata ƙaunar Kishiya ko kaɗan. Farkon mabuɗin waƙar yana nuna mana nau’in kishin da marubuciya ke ɗauke da shi shine kishi a kan wanda ta ke so, wato Mijinta. Ba ta aminta da kishiya ba samsam don haka ta kira ta da sunaye munana, kamar Tinkiya kuma ta kira ta Mummuna a cikin wadannan baitukan:

So mai son ki ‘yar yarinya,
To ya zan da halin kishiya?

Mijin ki ke so ko kishiya?
Har kin sani ‘yar dariya.

Bani amsa kar na gajiya,
Umh! Shi na ke so gaskiya.

Me yasa za ki afka rijiya?
Kishin mummunar kishiya.

To me ya gama ki da tunkiya?
Ta bar turke tana ta tafiya.

Ki bar ta tai ta yawon rariya,
Ai tsabata take ta had’iya.

Kishiya ga ‘ya mace duk irin kyawun halinta ba abar ƙauna ba ce don haka su ka kallafawa kan su cewa a zauna da haƙuri. Marubuciyar ta nuna wannan hali na mata na cewa zama da kishiya sai haƙuri cikin nasiha da jan hankali tare da nusarwar irin halin da rashin haƙurin ka iya jefa ‘ya mace idan ta gaza shi. Muhalli shahidin wannan tsokaci ya fito ne a waɗannan baituka kamar haka:

Koma gidanki ki ci nakiya,
Yaji nayo zuwa gidan Hajiya.

Kaicon kanki marar dauriya,
Kwanana nawa ina ta juriya.

Amma babu zaman lafiya,ina
Sai baƙin ciki nake had’iya.

Don Allah nai miki magiya,
Kar ki sa ‘ya’yanki cikin wuya.

Zaman aure shi ne moriya,
Ni ko iya tuntuni na gajiya.

Ki koma ɗakinki ki tausaya,
Gidan namu ba zaman lafiya.

Yaran da ki ka baro Mariya,
Kukan da ne ke yi kenan iya.

To,koma ki zauna lafiya,
Ai ko na fito Yaji tun jiya.

Kaico kin kwance tsintsiya.
Kin san sharrin Zafin zuciya.

Faɗa mu kai shekaranjiya,
Kaiya! Ki bar batun kwaramniya.

Ai ta doke ni da tsumagiya,
Bautar aure ibada ce sai dauriya.

A cikin waɗannan baituka marubuciyar cikin sigar hakukurtar da mata ta nuna cewa dukan gidaje na fuskantar matsala babu gidan da ya kuɓuta hatta gidan iyayen ita tauraruwar da ke cikin labarin da wakar ke ɗauke da shi.

Mun ga inda Uwar Mariya ke faɗa mata cewa ta koma gidan mijinta domin nan ma gidan na su babu zaman Lafiya. Hakanan waɗannan baituka sun fito mana da akasarin nau’in kishin mata kishi ne na kin yarda ko rashin haƙurin yin taraiya da wata cikin abin ƙaunarta, wato mijinta.

Samuwar Matsala sunna ce ta rayuwa amma ana iya samun galaba a kan kowane lamari maras dadi da haƙuri. Rashin Hakurin mace game da zaman aure abune da ka iya jefa yaranta cikin gararin rayuwa. Wannan ita ce nasihar da Uwar Mariya ke yi mata cikin saƙar waken wannan Marubuciya.

Sai dai duk da wannan nasiha da Uwa ke ma ‘yarta, gargadin ya zo a makare domin tuni Mariya ta kurɓi Ruwan Tumfafiya, baƙin kishi wanda ya munana ya angiza ta cikin nadama. Zaren wannan hange na mu na baiyana ne inda Marubuciyar ke warware shi cikin waɗannan baitukan:

Ai ko sai nai mata kurciya,
Bari yin aikin asarar dukiya.

Ai sai ta yi yawon duniya,
Kar ki kauce hanyar gaskiya.

Na daina ɗaukar murd’iya,
Kin san duk kumburin macijiya.

Ba ta iya kamo tsawon igiya,
Kar ki sammu kin ji ‘yar d’iya.

Sai na ga bayanta a duniya,
“Kai sannunku ma su tafiya.

Me ye ka ke gudu da hajijiya?
“Kishiyarki a daren shekaranjiya.

Ta yi fama da rashin lafiya,
Yau ta mutu da farar safiya.

Sai mu je ki wa kanki kariya,
‘Yan sanda aikinmu gano gaskiya.

Da me zan wa kaina kariya,
Kar a ce na rabata da duniya.

Ban mata komai ba ka jiya,
Bakina ya ja min zargin tsiya.

Sai mu je can ki amsa tambaya,
Har Kuka ya zo min a idaniya.

Yarinya kin biyewa zuciya,
Ta sa kin furta baƙar aniya.

Iya wajen faɗa shekaranjiya,
Na yi barazana don zuciya.

Zan rabata da zaman duniya,
Amma banda nufin kashe kishiya.

Wai kin tafka halin mikiya,
Kin kurɓi ruwan Tumfafiya.

‘Daurayarki wane ruwan maliya,
Sai dai Ilahu Sarkin gaskiya.

Mace ta faɗi wata mummunar Magana a kan kishiyarta ko aikata ma ta wani abu maras daɗi duka sananne ne ga kowa, idan an ji ma ba labari bane, kamar dai ka ce kare ya ciji mutum ne. Muna iya ganin irin wannan halaiyar ko da a labarin rayuwar magabata.

Misali lokacin da Manzo SAW ya auri Safiyyah, yayinda ya iso Madina sai Aisha RA ta bad-da-kama, ta fito domin ganin ta. Lokacin da su ka kusa isowa ga wurin da ta ke sai nan da nan ta yi sauri ta juya tana mai nufin komawa. Amma kuma Manzo SAW ya gan ta ya kuma gane ta, sai ya nufo ta cikin sauri ya riske ta. A cikin labarin da take bayarwa da kan ta Saiyada Aisha RA sai tace “lokacin da ya riske ni sai ya rike ni ya jawo ni gare shi sai ya ce da ni “Ya kika gan ta?” sai na ce “ Na ga Bayahudiya a cikin Yahudawa”.

Idan za ku tuna, Safiyyah ‘yar ƙabilar Yahudawan Bani Kuraiza ce. Bayan rundunar Musulmi ta sami galaba a kan su, an kama ribattun yaki da dama wanda Safiyyah tana cikin waɗanda a ka ribata. Ita kuwa ‘ya ce ga shugaban wannan ƙabila ta su. Manzo SAW ya aure ta tare da sanya ‘Yancinta shi ne sadakinta. Sun iso madina tare da ‘yan ƙabilarta waɗanda a ka kamo a matsayin ribatattun yaki. Wannan ne manufar maganar Aisha RA cewa ta gan ta, Bayahudiya a cikin Yahudawa.

Aisha RA ba ta daina jifan Safiyyah da wannan Kalma ta Bayahudiya ko ‘yar Yahudawa ba har sai da Manzo SAW ya karantawa Safiyyah abinda da za ta mayarwa da kishiyoyinta martini da shi.

Idan kin kishiya ya munana ga mace to ya kan angiza ta ga neman ranta ko da’awar kawar da ita dungurum wanda idan abin ya zo bisa katari sai ka ga baki ya yanka wuya. Wannan shine abinda ya faru ga Mariya kamar yadda Marubuciyar ta baiyanar cikin baitukan da su ka gabata. Idan kishi ga mace ya kai ga haka to ya munana hasali ma ba irin kishin ‘ya mace ba ne , neman rai ko lafiyar mutum saboda kishi ya fi yawa ga haliyar mazaje. Haka dai Malama Salamatu ta gabatar da wannan Mabuɗin Muhawara mai ɗauke da nishaɗi da ƙayatarwa cikin baituka 38.

Wanda ya fara gabatar da sharhinsa bisa wannan Muhawara ta Ruwan Tumfafiya shine Malam Habibiy wanda ke ɗauke da sunan adireshin yahoo na Honey Asal. Ya zo da martaninsa cikin baituka 13, waɗanda dukaninsu kamar goyon baya ne ga abinda da Marubuciyar ta gabatar. Ya buɗe martanisa ga yabo gareta tare da ƙarfafa nasihohinta kamar haka:

Sannu Salamatu Yar’uwa
Kin yi batun son gaskiya.

Kishi ya mamaye zuciya
Gami da baƙar jarabar tsiya

Me zai sa ki kassara Kishiya?
Ki raba ta da filin duniya

Mijin nan dai da kin ka ce
Ba shi ga dan goyon godiya

Dan kunama ne fa shi
Uban da zai maisheki Marainiya

Ruwayar Mata ce fa ku ji
Can a littafin su Masheriya

Wanda har halinsa ne haka,
Dominsa a ce mi ki tsinanniya?

Ki haƙuri ki zamto Fa’iza
Kwaɗayin ki sami rabauniya

Salame, Zubaida kun sam rabo,
Allah ya kai ku cikin Firdausiya

Rokon addu’arku ga Bintalo
Allah tsareta shiga ɗaukakkiya

Ta Spikin yarinya mai kwarjini,
Haƙuri da yawa ga tarin juriya

Sa’ade, Sa’a ‘yar Babani
Da ma ki zam gare su matashiya

Ni dai inai mu ku fatan arziki
Allah raba ku da sharrin Kishiya.

Malam Nasiru Yaro cikin baituka guda hudu kacal ya bi bayan Habibiy wajen yabawa Marubuciya tare da goyon bayar nasihar da ta gabatar cikin wannan Muƙala ta Ruwan Tumfafiya kamar haka:

Haƙiƙa kinzo da zancen gaskiya
Don ko baki shike yankan wuya

Kuma haƙuri shine maganin kishiya
Kai harma da mai gidan gaba ɗaya

Da fatan Matayen mu kulliyya
Za su ɗauki nasiharki muhimmiya

Da fatan Allah yayo miki buɗiya
Ta fasaha tare damu gaba ɗaya

Shehin Malami, Baharul Ilmi, Malam Fatuhu Mustapha hakanan shi ma ya zo da gudunmawar baituka goma duka cikin goyon bayan Marubuciya. Cikin nuna ƙwarewar rubutun waka mai kayatarwa, Malamin ya ƙarfafi nasihar Marubuciyar da waɗannan baituka:
Madalla Salamatu kinyi ‘ya
Kin tantance mana gaskiya

Akan waƙar ki ta kishiya
Ku mata sai kuji gaskiya

Sai ku taru ku zauna lafiya
Banda jayayya ɗan kishiya

Ku mata nai muku magiya
Kuji tsoron Allah shi daya

A zaman aurenku da kishiya
Ƙwaila da budurwa bai daya

Tsohuwa, zawara ma duk ɗaya
Ai zaman aure ba fariya

Ku zo gangan mu rike igiya
Wadda yai horo wahadaniya

Mui zaman aure ba wariya
Na gode Sarki Ilahu gaba daya

Ahadun sarkin nan shi daya
Warin masaki wahadaniya.

In sanya salatin Mustapha
Dan Aminatu Manzon gaskiya
Bayan waɗannan gudunmawa daga waɗannan marubuta uku da su ka bayar bisa wannan muƙala cikin baituka 27 gabadayansu, sai alkalamin Marubuciyar ya juya ga barin dama ya kaikaice hagu. Ban san menene dalilinta na barin bigirenta na yiwa kanta da ‘yanuwanta mata nasihar kishiya ba sai ta koma ga ‘yar adawa zalla.
Mai yiwa a nan muna iya cewa abin boye ne ya fito fili ta baiyana kanta cikin Lisanil-hali. Tana kallon kamar za a yi mata kuskuren fahimtar cewa tana son Kishiya ko ta nuna tausasawa gare ta, don haka ta dawo da waɗannan baituka domin goge zaton da take gudun a yi ma ta dangane da Kishiya. Muna iya ganin yunƙurinta cikin waɗannan baituka inda take cewa:

Kar ku ji na ƙalubalanci kishiya,
Ku za ci ko sonta nake a zuciya.

In da za ku yi yo mani tambaya,
Sai in ce ban sonta gaba-daya.

Da maigidana yai man kishiya,
Gwamma kullum yai man bulaliya.

Fatuhu na san za ka yi yo dariya,
Habiby da Nasir ko sai sun rausaya.

Ta yaya kaza za ta so mikiya,
Bare ta ɗauketa aminiya.

Ta ya Aku zai ƙawance da mujiya,
Wacce ba ta son hira gaba-ɗaya.

Kai tsaye bayan waɗannan baituka sai ta garzaya neman taimako daga wasu gumakanta gami da ƙawaye cikin waɗannan baituka kamar haka:
Baba prof jiye min zancen kishiya,
Wacce duhunta ya fi duhun rijiya.

Makarantar Hausa ba zancen zaulaya
Ka san zafin kishiya ya fi na bulaliya.

Binta Rabi’u nasiha na yo kan kishiya,
Su maza na son in maisheta aminiya.

Umma Ali kin ji zancen nan na kishiya,
Mazan majalisar na sonsa gaba-ɗaya.
A cikin Zubin lisanul Hali Marubuciyar ta tabbata cewa ta na kin Kishiya. Ta ƙalubalanceta, ta zage ta, ta munanata gami da ambatonta da munanan kalamai da siffofi munana inda take kiranta da kaza, sannan ta ce mata mujiya. Siffanta ko wacce irin mace da wadannan siffofi ba yabo ba ne a harshen Hausa.

Mun san kaza da rashin godiya, don haka ma bahaushe ki siffanta mutum marar godiya da Kaza ci ki goge bakinki. Anan marubuciyar na son nuna mana cewa kishiyar ba mutuniyar kirki ba ce, saboda halinta na rashin godiya. Hakanan ma mujiya an san ta da baƙin Jini a cikin tsuntsaye hakanan ma Kishiya take a cikin jinsin mata.

Sai dai wannan juyin juya hali na alƙalamin Marubuciyar ya sake karkato da hankalin abokan muhawararta musamman ma Malam Habibiy. Muna iya ganin inda shi ma ya karkatar da alkalamin nasiharsa zuwa ga ita marubuciyar cikin baituka goma sha-biyar [15]. A farkon martaninsa ya nuna mamakinsa na irin juyin da Marubuciyar ta yi cikin kankanin lokaci. Yayi ƙoƙarin nuna mata arzikin rayuwa ƙaddara ce, kowa abinda aka rubuta ma sa shi zai ci, ba zai ci rabon wani ba tare da jawo hankalinta bisa Sunnar Aure da kokarin yin koyi da magabata Ababan koyi cikin biyar Aure.

Haba Salamatu Jaruma
Me ya kai ki ga baud’iya
 
Kishiya ce ko ‘yar’uwa
Allah raba ki da tsallen tsiya

Arzikinta da na ki duk da ban
To ina gaminki da bulaliya
 
Sunnar Ma’aiki Rabbana
Sa’ade rike ta da godiya
 
Dan Amina Manzo Mustapha
Matansa sun riki kishiya
 
A zamansu ba cuta ko kadan
Sun nuna hanya ta zumunciya
 
An ce ki zam koyi da su
Sune fa jagorarki gaba ɗaya
Malam Nasiru Yaro ya ari alƙalamin Habibiy inda shi ma ya karkatar da nasiharsa ga Marubuciya tare da nuna mata alherin Kishiya. Yana faɗakar da ita cewa ko ba komai ta sami abokiyar hira da shawara hakanan ma za ta sami mataimakiya cikin sha’anin aiyukan gida na yau da kullum.

Waɗannan raddi da abokan muhawarar su ka yi ma Marubuciya ya sake yi mata tsinke inda ta zabura ta yiwo tumbuɗin baituka 24 don kare matsayinta. A cikin kariyarta ta nuna rauninta game da yin haƙurin Kishiya tare da jawo hankulanmu cewa manyan bayi abin biya su ma sun gaza ga ɗaukar kishiya. Farko ta fara da cewa Allah SWT da kansa ya ki kishiya to ita wacece?

Sannan daɗin daɗawa, Khadija Matar Manzo SAW da A’isha RA uwar Muminai da Saratu mai ɗakin baban Ambiya’u dukaninsu sun gaza jurewa kishiya. Sai da duk da waɗannan dalilai da take ganin za su zame mata kariya Malam Habibiy bai bar ta ba sai da ya biyo baya yana kunce duk ƙullin da ta yi daya bayan daya, kamar yadda fashin baƙin zai baiyana mana nan gaba kaɗan. A baituka sha-biyu [12] na farkon martaninta Marubuciyar ta gabatar da dukkan uzororinta kamar haka:
Salamma gareku masoya kishiya,
Tawassali ga Allah Sarki ɗaya.

Salatinmu ga Manzon angon Mariya,
Da alaye nasa sahabu gaba ɗaya.

Ta’aliki zan kuma bisa wakar kishiya,
Ni dai ga kishi ban iya in yo juriya.

Allan da yi yo mu duk gaba-ɗaya,
Ya yi horo da hani kar ai mar kishiya.

Haka Manzo Rasulu imamul ambiya,
Duk da matansa sun zamna da gaskiya.

Nana Khadija ta rok’i Allah Sarki ɗaya,
In manzonmu ya tashi yo mata kishiya.

To ranar ranta ya barta ta sakaya,
Wato ta zam ba ita a filin duniya.

Uwarmu kenan Sayyida bare ni ɗiya,
Maza ku ce min na aminta da kishiya.

Yayin da Khadijan ma ba ta duniya.
A zahiri A’isha tai kishinta da zuciya

Haka Saratu ta kasai wa kishi juriya,
San da ta halastawa Mujinta kishiya.

Ita ta ba shi Hajaru da kyan zuciya,
Amma kishi ya hanata ta yo dauriya.

Ahalin Annabi Ibrahimu abin biya,
Bare ni Salamatu marar dauriya.
Uzurin Marubuciya na kin kishiya saboda Allah SWT ba ya son kishiya gare shi. Sai Habibiy ya kalubalance ta da wadannan baitukan:

Allahu Rahimu Sarki Rabbana,
Lalle kam ba ya son Kishiya.

Salamatu kauce, wane fa ke,
Ai babu kamarsa a fadin duniya.

Babu mai koyi da kama ta sa,
Ya hore ki da koyin ambiya.

A jarabtar bayi babu kama ta su,
Mai bin su dole ya bar sharholiya.

Koyi da su ba gadon barci bane,
Sai ki dauki shirin hawa garwashiya.

Wahalarki ta zam miki guzzuri,
A gobe ki sha ni’imar Firdausiya.

Idan hakane karshen juriyar,
Allah daɗo mi ki dubban Kishiya.

Nasiha ce gareki Sa’a ‘yar babani,
Ki rika don tafi buhun zinariya.

A cikin waɗannan baituka yana nusar da ita cewa ba a yin koyi da Allah sai dai a yi koyi da Annabawa da kuma salihan bayi. Kuma koyi da su ba abu ne mai sauƙi ba, duk mai aniya to dole ne yayi damara domin zai taka garwashi ne cikin rayuwa. Amma idan yayi haƙuri ya jure to wahalarsa nan gaba za ta zama dadi gare shi. Ya kare da cewa wannan nasiha gareta idan ta riƙe ta, to ta fi buhun zinariya.

Da’awarta na cewa Saiyada Saratu ta yi kishi da baiwarta Mahaifiyar Annabi Isma’il Alaihissalam balle ita. Wannan uzuri da alama Marubuciyar na yin ishara ne ga ruwayar Waqidiy wacce ya samo ta daga Muhammad bn Salih, daga, Sa’ad bn Ibrahim, daga Amir bn Sa’ad daga Babansa cewa: Saratu ta kasance a hannun Annabi Ibrahim AS tsawon lokaci babu haifuwa.

Lokacin da ta ga zamani ya tsawaita sai ta ba shi kyautar baiwarta Hajara ko Allah ya arzurta su da samin haifuwa. Haka ce kuwa ta faru, Hajara ta haifi Annabi Isma’il AS. Daga nan sai kishi ya zo wa Saratu ta ji ba ma ta son ganin Hajara har ma dai ƙarshe ta yi rantsuwa sai ta yanke gabobi uku a jikin Hajara.

Daga nan ne Annabi Ibrahim AS yace da ita bari na fada miki yadda za ki kuɓuta daga rantsuwarki, sai ta ce kamar yaya ke nan? Sai ya ce da ita, kawai ki huda kunnuwanta guda biyu sannan ki yanki wani abu a gabanta [kaciyar mata] idan kin yi haka kin cika rantsuwarki. Sai ta yarda ta aikata hakan. Yayinda a ka yi wa saratu huji a kunnuwanta, ita kuma sai ta sami ɗankunne ta rinƙa maƙalawa, sai Saratu ta ga ta sake yin kyau sosai sai kishinta ya sake ƙaruwa har ma dai ta ji ba ta son zama da ita gaba ɗaya.

Ganin halin da take ciki sai Annabi Ibrahim AS ya shiga damuwa domin tausaya ma ta, daga bisani Allah SWT ya umarce shi da ya ɗauke ta ya kai ta inda Haramin Makka yake a yanzu. (Haka Ibn Asiyr ya faɗi wannan ƙissar a cikin littafinsa mai suna AL-KAMIL juzu’i na farko a wajen shafi na 103). Marubuciyar ta kara uzurorinta da maganar Khadija RA da kuma Aishatu Ummu Mumunina matayen Manzo SAW. A bisa waɗannan dalilai da ta bijiro da su Habibiy ya ƙalubalance ta da waɗannan baituka:

Salamun ke mai tsoron Kishiya,
Tabbas kin kurbi ruwan Tumfafiya.

Adawarki ga karɓar Kishiya,
Ya sa ki bige da fagamniya.

Kin ce Saratu babar Ambiya,
Ta kasa haƙurcewa Kishiya.

To ki aikata aikin Sarah man
Ko ya zam mu kira ki sharifiya.

Ki tallafi dan nan Maigidan
Ke ma ki ba shi taki Aminiya.

Koko ma riko ‘yar aikin gida,
Wacce ke kika ɗauketa hadimiya.

Daga baya idan ma kin so kice,
Lalle ne ya sake ta ɓarauniya.

Salatinmu ga mai dakin Ambiya
Wacce ta mai da Hajara ‘yantacciya
Sannan game da matayen manzo SAW kuwa wato Khadijatul Kubra da Aishatu RTA sai Habibiy ya doke ta da waɗannan baitukan:

Manzonmu ya girmama Kubra,
Ya kaɗaita ta bai mata Kishiya.

Hadizan Manzo amma ta kuɓuta,
Daga inkarinsa ya yi yo mata Kishiya.

A’i Barra’atu ‘yar gatan Rabbana,
Kubutatta take har can a samaniya.

Humaira Barra ‘yar Siddikuna,
Ki yo haƙurin zamanta da Kishiya.
A ƙarshen Muhawarar Marubuciyar da alama ta dan sakko kuma ta karkata ya zuwa nasihohi da jan hankalin da abokan muhawarta tata su ka yi mata duk da cewa ta yi inkarin dalilan da Malam Nasir Yero ya kawo mata cikin baitukansa na ƙarshe guda biyar.

Cikin ragowar baituka sha-biyun ƙarshe na martaninta marubuciyar ta baiyana irin ko nau’in kishin da take ɗauke da shi. Ba ta bambamta da akasarin mataye ba a nan wato kishin akasarin mata kishi ne a kan abin ƙauna ba kishi domin abin ƙauna ba. Kar na yi riga-malam-masallaci, bari mu ji abinda take cewa cikin baitukan:
Ku dai ku ce kar a bi zafin zuciya,
Har a kurɓi Ruwan Tumfafiya.

A yi zama na amana ba ‘yar kurciya,
Ba dambe ba duka da tsumagiya.

In mace na son muji dole ta guji kishiya,
In ko bata son shi ya aure matan duniya.

Fatuhu da Habiby kun shirin yo kishiya,
Gun matanku shi sa ku ke min zaulaya.

Nasir gwamma nai aikin yasar rijiya,
Da in bar aikin gida yasa ai min kishiya.

Ni dai maigidana bai min kishiya,
Ya ce ko da na bar nan duniya.

Ba mai maye gurbina a cikin zuciya,
Bare ma ya so wata hatsabibiya.

Idan zai aure ma to burtuntuna,
Abadan ba ta zame mar abokiya.

Addu’arku wayyo niya ‘yar d’iya,
Kar a min k’wark’wara madadin kishiya.

Ni ‘ya su ina zan shiga rannan duniya,
Tunda ban da ikon in yi yo tirjiya.

Sai dai na rok’i Ilahu ya sanyaya,
Jalla ka ban ikon na yi yo dauriya

Da haka Marubuciyar ta kawo ƙarshen wannan muhawara ta Ruwan Tumfafiya wacce ta ɗauki hankulan makaranta da dama kana ta ja hankulan masu sharhi irin su Malam Habibiy, Malam Fatuhu Mustapha da Malam Nasir Yaro. Ta Karkare da tabbata a matsayinta na kin kishiya babu sauyi duk da karbar nasihar da ta yi wanda ya sauko da ita cewa a yi kishi cikin haƙuri da zaman lafiya kar a karkata ya zuwa kishi mummuna.

Sai dai a ƙarshen wannan Muhawara mai karatu zai so ya ji wanne kishi ne mafi kyawu a cikin nau’ikan kishi guda biyu da a ka bijiro da su tun a farkon wannan muƙala. A nan zan iya cewa ai ko shakka babu mafi alherin kishi shine kishi don abin kauna. Shine kin wani mummunan abu ya sami masoyinka wanda ke angiza ka kai masa ɗaukin kariya ranka da dukiyarka.

Babu kishi maɗaukaki abin yabo fiye da wannan kishin. Amma kishi a kan abin kauna wannan an fi son shi tsakanin bawa da mahaliccinsa ko cikin lamarin addini da ‘yanuwantakar musulumci, wanda duka na komawa ne cikin sha’ani addini da ibada. Idan cikin lamarin addini ne babu laifi ko da ya tsananta amma idan kishi a kan masoyi ya tsananta ba bisa uzurin addini ba to wannan ya munana. Ya kan kai mutum ficewa daga addini dungurum ko kuma ya tura shi cikin Kaba’ira. Da yawa irin wannan ce ke faruwa ga matayenmu har su ke kai kansu gidajen bokaye inda a ke sa su aikata abubuwan dake da hatsari ga Imaninsu. Akwai misalai biyu mabanbanta da zan iya bayarwa anan kamar haka:

Na farko ya faru a zamanin Halifanci Saiyidina Umar bn Khattab RA. An kawo masa wani mutum da ake da’awar ya kashe wani bayahude sai yake tambayarsa mai ya kai shi ga aikata wannan mummunan aiki? Sai mutumin nan ya ka da baki ya ce ma sa ya Amirul Mumunina, Abokina wane ya fita tare da rundunar Jihadi sai ya bar min wasicin kula da iyalinsa. Sai labari ya zo gareni cewa wannan bayahuden yana rabawa zuwa gidan, don haka ni kuma na yi masa kwantan bauna har sai da ya zo, na ji shi yana tafe yana rera waɗannan baitukan:
(Ma’ana)
Wani Musulincinsa ya yaudarar min da shi
Na wayi gari dakin amaryarsa dare guda

Bisa kirjinta gareta nai kwanci cur dare
Shi ko ya maraice ga bakarara ba gida

Kai ka ce runduna ce take dosar runduna
Jiki na raurawa kuma ga kirji na zunkuɗa.

Ni kuma da jin haka sai na fito daga inda nake ɓoye na kashe shi. Jin wanna labari sai Saiyidana Umar RA ya watsar da karar, ya kuma wofintar da jinin bayahude. Babu abinda ya kai wancan mutum kashe bayahuden face kishin ɗan’uwansa cikin musulumci kuma abokinsa. Kishi cikin addini abin yabawa ne tunda har ta kai a na iya wofintar da jinin da a ka zubar a kansa. Wannan shine misali abin yabawa cikin kishi domin masoyi.

Kishi kuma abin tsangwama a kan masoyi shine wanda kan angiza mutum ga aikata aikin da ya fita daga horewar shari’ah. Misalin irin wannan kamar abinda ya faru ga Dikul-Jinni. Yana da wani yaro bawa kyakkyawan gaske da yake son sa sosai, da kuma wata kuyanga ita kyakkyawa da ta kama zuciyarsa. Wata rana ya shigo sai ya sami yaron nan nasa da wannan kuyanga rungume su na sumbatar junansu. Sai kishi ya kama shi, gabadayansu sai ya sa wuƙa ya yanke su. Irin wannan kishin ya munana domin ya angiza mai shi ga tsallake haddin shariah zuwa aikata kisa wanda kaba’ira ce mai girma. Shi ya sa za ka samu cewa bayin Allah Mumunai kan yi kaffa kaffa a irin wannan kishin domin indan a ka saki linzaminsa ba tare da ragamar Imani ba ya kan tsallake gona da iri har ya zama mushiriki. Saboda akasarin soyayya tsakanin bawa da Mahaliccinsa a wannan gwadaben take kaikawo.

Tankaɗe:
An gabatar wannan muhawara dukaninta a cikin baituka 147 bisa kiyasin gudunmawar dukan taurarin muhawar kamar haka:
SALAMATU ADAMU – Baiti – 74
MALAM HABIBIY – Baiti – 52
MAL. NASIRU YARO – Baiti – 11
MAL. FATUHU MUSTAPHA – Baiti – 10
Jumlar Baituka = 147

A ƙarshe cikin tsokacinmu muna iya cewa:

i. An yi muhawarar cikin tsafta da fahimtar juna. Taurarin sun nuna hankali da girmama juna, kuma akwai alamar sanaiya tsakaninsu ganin yadda wani lokaci ita kan ta marubuciyar kan ja su da tsokana.

ii. Hakanan akwai alamar zurfin bincike da ilmi mai ƙwari cikin kalamansu ganin yadda da yawa baitukansu na dacewa da nassoshi ko wani bahasin ilmi mai zurfi. Muna iya ganin haka a wurare da dama cikin baitukan Marubuciyar, Habibiy da Malam Fatuhu Mustapha.

iii. Duka muhawar ta ƙayatar sosai sai dai muce Allah ya ƙarawa Marubuciya basira tare da waɗanda su ka taimaka mata cikin wannan Muhawara.

KHALID MUSA,
08039130128, 09067612302
[email protected]