Saƙon ta’aziyya: Buratai ya jinjina wa Attahiru

Daga UMAR M. GOMBE

Tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Ambasada Tukur Buratai (Lt Gen Rtd) ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin rasuwar magajinsa, Lieutenant General Ibrahim Attahiru, da sauran jami’an da haɗarin jirgin sama ya rutsa da su a ranar 21, Mayu, 2021 a garin Kaduna.

Buratai ya bayyana kaɗuwar tasa ne a saƙon ta’aziyya da ya miƙa, tare yin amfani da wannan dama a madadinsa da iyalansa wajen miƙa ta’aziyyarsa dangane da wannan babban rashi ga Shugaban Ƙasa da iyalan marigayan, Ministan Tsaro, Shugaban Rundunanr Sojijin Sama ta Nijeriya da ma Nijeriya baki ɗaya.

Ya ce wannan ibtila’in ya kaɗa shi sosai, tare da bayyana hakan a matsayin babban al’amari ga ƙasa, sabida a cewarsa Lieutenant General Ibrahim Attahiru tare da jami’an da suka rasun manyan ma’aikata ne waɗanda suka bada gagarumar gudunmawa ga ƙasa.

“Na ji zafin faruwar wannan ibtila’in duba da cewa hakan ya shafi ƙoƙarin da magajina wanda ya zage damtse wajen yin aiki babu kama hannun yaro tun bayan da ya zama Babban Hasfsan Hafsoshi.

“Yana gab da kai Nijeriya ga gaci a fagen yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro inda wannan mummunan al’amari ya auku gare shi.

“Ban yi shakka ba dangane da ƙwazonsa saboda ya yi aiki a ƙarƙashina a matakai daban-daban wanda hakan ya sanya shi cancantar riƙe muƙamin da aka miƙa masa,” in ji Buratai

Ambasadan ya kuma yi kira ga Sojojin Nijeriya da su duba sannan su ɗora daga inda marigayan suka tsaya dangane da sha’anin bai wa ƙasa tsaro.

Ya ƙarasa da cewa abin alfahari ne ganin yadda marigayan suka rasa rayukansu wajen yi wa ƙasarsu hidima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *