Saɓa ƙa’ida: Tiwita ta goge saƙon Shugaba Buhari

Daga BASHIR ISAH

Sakamakon abin da ya kira da saɓa wa dokokinsa, kamfanin Twitter ya share wani saƙon da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya yi barazanar yin maganin waɗanda suka gagara ɗaukar izina daga yaƙin basasar da aka yi a Nijeriya.

Rahotanni sun nuna da alama dai kamfanin ya goge saƙon Buharin ne bisa zargin saɓa dokokinsa.

Cikin saƙon da ya wallafa a ranar Talata wanda bai yi wa Twitter daɗi ba, Buhari ya ce, “Galibin waɗanda ke nuna rashin ɗa’a ba su da masaniyar irin ɓanar da hasarar da aka tafka yayin Yaƙin Basasar Nijeriya.

“Mu da muka shafe watanni 30 a filin daga muna gwabza yaƙi, za mu tafiyar da su ta hanyar da ta dace.”

Saƙon da Buhari ya wallafa martani ne ga hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa wurare mallakar gwamnati a yankin Kudu-maso-gabas.

Sai dai saƙon ya harzuƙa wasu masu amfani da soshiyal midiya inda suka yi ta kumfar baki tare da nuna cewa saƙon Shugaban Ƙasar barazana ce kai tsaye ga al’ummar Kudu-maso-gabas na Nijeriya.

A cewar jaridar The Nation, wannan al’amari ya sanya da daman masu amfani da soshiyal midiya suka kai ƙarar shafin Shugaba Buhari ga kamfanin na Twitter.

Kamfanin Twitter ya bayyana cewa duk wani saƙo da aka wallafa wanda ya saɓa dokokinsa, yakan buƙaci mutum ya goge saƙon kafin samun damar ci gaba da wallafa saƙonni a shafin nasa.