Sababbin hafsoshin Buhari

An daɗe ana kira da roƙo ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauya manyan hafsoshin sojan ƙasar nan masu jagorancin rundunonin tsaro, amma ya na ƙi. Sai da ta kai Majalisar Tarayya ta zartar da ƙudirori a kan lallai ne Shugaban ya kori hafsoshin, amma dai maganar ta wuce ta bayan kunnen sa. Dalilai biyu su ka sanya aka riƙa yi masa wannan kiran. Na farko shi ne, wa’adin hafsoshin ya wuce, har ma ana ganin sun fara cin wa’adin wasu hafsoshin domin tun a cikin 2015 aka naɗa su. Dalili na biyu kuma shi ne gazawar da ake ganin sun yi wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke damun ƙasar.

Wannan dalilin na biyu ya fi damun kowa. Matsalar rashin tsaro ta taɓarɓare ta yadda kusan ko’ina a ƙasar babu inda talaka ke iya barci da idanun sa biyu a rufe. A kullum sai ka ji an aikata wata ta’asa a wani wuri. A yankin Arewa-maso-gabas babu abin da ya fi damun jama’a kamar matsalar Boko Haram. Waɗannan ’yan ta’addar sun hana kowa saƙat. Ba su bar jami’an tsaro ba ballantana farar hula. Duk da ƙoƙarin da dakarun mu ke yi a bakin daga don ganin bayan wannan ƙungiyar, hare-haren ba su gushe ba. Yaƙin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

A yankin tsakiyar Nijeriya kuma ana fama da satar mutane da kashe-kashen da ake yi a ƙauyuka da dazuzzuka, ga kuma rikicin Fulani makiyaya da wasu ƙabilun. A Arewa-maso-yamma ma satar mutane da dabbobin su da auka wa ƙauye ko gari da kisa da ’yan bindiga ke yi abin ya ta’azzara. Arewa gaba ɗayan ta ta zama wani babban filin yaƙi inda a kullum sai an rasa rai. Idan ka nausa ka yi kudu, nan ma babu zaman lafiya. Ana rikice-rikice da kashe-kashe da ƙone-ƙone.

Nijeriya ta zama wata irin ƙasa wadda ke fuskantar barazanar hargitsewa saboda halin rashin tsaro. An yi rashin dubban rayuka da dukiya ta biliyoyin naira. Babban abin damuwar ma shi ne yadda talakawa da dama su ka sadaƙar, su na ganin cewa gwamnati ba ta iya kare su tare da dukiyar su, musamman da ake cewa da haɗin bakin wasu ɓatagarin jami’an tsaro ake aikata wannan ta’asa.

A yayin da ake fama da wannan badaqala, gwamnati na ta danqara wa hukumomin tsaro maƙudan kuɗaɗe domin a shawo kan matsalar. Amma kullum jiya iy yau, kamar ma ƙara zuga abin ake yi. Su kuma shugabannin tsaron, kullum ji ake su na cewa wai sun kusa kawo ƙarshen matsalar. A wajen talaka, duk cigaban mai ginar rijiya ne.
Abin da ya fi damun jama’a shi ne ƙyalen da Buhari ya yi. Har ta kai ga cewar wasu na faɗin Buharin da su ka sani a zamanin mulkin soja da ya yi da kuma irin aƙidar da ya riƙe a zamanin zaman sa na farar hula kamar ba shi ba ne wannan. Wancan Buharin, zafi gare shi; wannan kuwa sanyi gare shi kamar ƙanƙara.

A dalilin irin wannan kallon da ake yi wa gwamnati ne ya sa kowa ya yi murna ranar Talata da aka samu labarin cewa Shugaban {asa ya sauke manyan hafsoshin sojan sa, wato bayan ya ce su miƙa takardun kenan. Haka kuma sun yi na’am da sababbin naɗe-naɗin da ya yi. Duk da yake tun tuni aka so ya yi hakan, kusan kowane ɗan Nijeriya ya yi murna da jin cewa an dai yi canjin, domin da babu gara kaɗan. Yanzu kusan kowa gani ya ke kamar an kawo wata gava inda za a yi maganin matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.

Mu ma a jaridar Manhaja mun yi marhabin da sauyin da aka samu na shugabancin rundunonin tsaro na soja. A wannan jaridar mun sha kawo rahotanni kan yadda matsalar rashin tsaro ta yi wa Nijeriya katutu da yadda aka kasa shawo kan ta. A ganin mu, sauya shugabannin da aka yi zai iya zama sanadin magance matsalar.

To, amma fa ana wata ga wata. Kada mu manta, waxannan sababbin manyan hafsoshin da aka naɗa su ne dai su ka aiwatar da yaƙi da matsalar rashin tsaron a ƙarƙashin jagorancin su Janar Tukur Buratai. Tare da su ne su Buratai su ka riqa shawarta yadda za a yi. Abin da kawai Shugaba Buhari ya yi shi ne ya tsinke kawunan rundunonin tsaron ne, su kuma waɗannan hafsoshin da ake yi wa kallon sababbi su ka maye gurbin su. Don haka ayar tambaya ita ce: rawar za ta sauya tunda kiɗan ya sauya kuwa?

Ganin sauyi shi ne fatan kowane ɗan Nijeriya daga wannan canji da Buhari ya yi. Duk da yake sababbin shugabannin rundunonin sojan tare da su aka yi jagorancin baya, yanzu fa su ne jagororin. Ba za su karɓi oda daga hannun wani in ba Buhari ba; su ne za su zauna su shawarci Shugaban Ƙasa kan dukkan abin da ya dace a yi. Don haka ake so a ga sauyin kamun ludayi daga gare su. Shi ma Buharin haka ya buqata daga gare su a ganawar da ya yi da su shekaranjiya.

Tilas ne su fito da sababbin hanyoyi na tunkarar matsalar tsaro, domin kuwa hanyoyin da ake ta bi kawo yanzu duk ba su ɓulle ba. Kamar yadda su ka sani, alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ya gada daga gwamnatin Jonathan ya na daga cikin manyan alƙawura uku da Shugaba Buhari ya yi wa ’yan Nijeriya har su ka zave shi; sauran biyun su ne yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma gyara komaɗar tattalin arziki. To su taimaka a cika wa jama’a wannan alƙawarin.