Sabon Alƙalin Alƙalai, Ariwoola: Mutumin da ya soma makaranta bayan shekara ɗaya da haihuwa?

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Nijeriya ci gaba da ce-ce-ku-ce da kuma nuna mamaki kan lamarin shekarar haihuwa da ta soma makaranta kamar yadda ya shafi sabon Alƙalin Alƙalai na ƙasa, Jastis Olukayode Ariwoola.

Jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin muƙaddashin Alƙalin Alƙalai, takardun bayanin kai da Ariwoola ya miƙa sun nuna an haife shi ne ran 22 ga Agustan 1958 a Jihar Oyo sannan ya fara makarantar firamari a 1959, wato bayan shekara ɗaya tak da haihuwansa ke nan.

Kazalika, takardun nasa sun nuna ya halarci Muslim Modern School daga 1968 zuwa 1969, kana ya tafi sakandaren Ansar-Ud-Deen high school, da ke yankin Saki, Jihar Oyo.

A ranar Litinin da ta gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alƙalin Alƙalai na riƙon ƙwarya biyo bayan murabus da tsohon mai riƙe da muƙamin, Mai Shari’a Tanko Muhammad ya yi bisa dalilai na rashin lafiya.

Ana sa ran Ariwoola ya ci gaba da riƙe wannan sabon muƙamin nasa har zuwa lokacin da ɓangarorin da lamarin ya shafa za su tabbatar da naɗinsa.

Ariwoola ya yi karatunsa na lauya ne a Jami’ar Ife wadda a yanzu ta koma Jami’ar Obafemi Awolowo, inda ya kammala a 1980. Bayan nan da shekara ɗaya ya samu zama cikakken lauyan Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *