Sabon Gwamnan Kano ya yi naɗe-naɗen farko

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf – Abba Gida Gida, ya sanar da naɗin rukunin farko na ma’aikatan da zai yi aiki tare da su.

Naɗin na zuwa ne awanni bayan shan rantsuwar kama aiki.

Sanarwar da ta fito ta bakin mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta nuna an naɗa tsohon Shugaban TETFUND, Abdullahi Baffa Bichi a matsayin Sakataren Gwamnati, sannan Hon Shehu Wada Sagagi a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati.

Sauran sun haɗa da; Dr Farouq Kurawa Babban Sakatare na musamman, Hon Abdullahi Ibrahim Rogo a matsayin Shugaban Tsare-tsare, yayin da aka naɗa Sanusi Bature Dawakin Tofa a muƙamin Sakataren Yaɗa Labarai.

Sanarwar ta ce, “Naɗin ya soma aiki nan take, kuma waɗanda aka naɗan an zaɓe su bisa cancanta da biyayya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *