Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato
Sa’o’i 24 shan rantsuwa Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr. Ahmad Aliyu ya soke naɗe-naɗen da gwamnatin Aminu Tambuwal ta yi da ƙarin girma ga ma’aikatan jihar bayan 19 ga watan Maris, 2023.
Bayan haka, Gwamna Ahmad ya soke dukkanin canza sunayen manyan makarantun jihar da duk abin da ke da alaƙa da shugabannin gudanarwar makarantun, kamar yadda bayanin ya ce dukkaninsu, sun koma sunayensu da aka sansu da su a baya.
A bayanin da ya yi wa manema labarai, kakakin gwamnan, Abubakar Bawa, ya ce, Gwamnan ya ce za a sake wewayar naɗe-naɗen sarautun da tsohon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi domin muradun al’umma.
“Sabuwar gwamnatin Ahmad ta soke dukkanin Kantomomin Ƙananan Hukumomi 23 da Kwamitocin riƙon ƙwarya, tare da umartar Kantomomin da su miƙa ragamar mulki ga Daraktocin Mulki na yankunansu.
“An kuma soke dukkanin Shugabannin Hukumomi da Ma’aikatun gwamnati nan take in ji Kakakin Gwmanan, inda yaƙara da cewa, sun kuma soke dukkanin filaye da abinda ke kama da hakan wanda gwamnatin da ta gabata ta yi.
“Kazalika, gwmanatin ta dakatar da dukkanin gwanjon kayan gwamnati da aka yi, tana mai cewa za ta sake dubawa.”
Idan dai za a iya tunawa, kwanaki ƙalilan gabanin kammala wa’adin mulkinsa, tsohon gwmanan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi wasu naɗe-naɗe da ma sauye-sauye a lamurran jihar.