Sabon Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa ya buƙaci al’umma su riƙa mara wa shugabannin su baya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Sabon zaɓaɓɓen shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa da aka sake zave karo na 3 Honorabul Ibrahim Balarabe Abdullahi ya taya al’ummar jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya murnar sake zagayowar ranar dimukaraɗiyya na bana wadda aka gudanar ranar Litinin 12 ga watan Yunin shekarar 2023 a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

Honorabul Ibrahim Balarabe Abdullahi ya taya ‘yan Nijeriya murnar ranar ne a wani takardar sanarwa na musamman da mataimakinsa na fannin yaɗa labarai Alhaji Jibrin Gwamna ya sanya hannu aka raba wa manema labarai ciki har da wakilin mu a birnin Lafiya.

Kakakin majalisar dokokin ya ce ba shakka kawo yanzu shugabannin ƙasar nan a duka matakai sun cancanci yabo idan aka yi la’akari da sadaukarwa da suke yi akoyaushe don samar da cigaban ƙasar nan baki ɗaya.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya su cigaba da bai wa shugabannin su cikakken goyon baya don ba su damar cigaba da samar musu da waɗannan ribobin dimukaraɗiyya.

Ibrahim Balarabe Abdullahi ya kuma yi alƙawari cewa zaɓinsa karo na 3 da aka sake yi a matsayin shugaban majalisar dokokin ta jihar Nasarawa zai ba shi damar cigaba da yin aiki tukuru wajen tabbatar al’ummar jihar baki ɗaya sun cigaba da samun ribobin dimukuraɗiyya a duka fannonin rayuwa.

A makamancin haka, Jam’iyyar APC mai ci a jihar ta bayyana vangaren sabon kakakin majalisar dokokin jihar da ya ƙunshi ‘yan majalisar dokokin su 12 a matsayin ainihin waɗanda jam’iyyar ta amince da zaɓen su na shugaban majalisar dokokin ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban, Honorabul Ibrahim Balarabe Abdullahi.

Hakan ya fito ne ta bakin shugaban jam’iyyar a jihar, Mista John Mamman a wani sanarwa ta musamman da ya gabatar wa ‘yan jarida.

Haka ita ma gwamnatin jihar tuni ta bayyana shi Ibrahim Balarabe Abdullahi a matsayin wanda aka san da shi kuma za ta cigaba da hulɗa da shi a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin karo na 3.

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne aka samu rigima a zaɓen sabon shugaban majalisar dokokin jihar inda aka samu ɓangarori 2 wato ɓangaren shi Balarabe Abdullahi da Daniel Ogah Ogazi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *