Sabon rikicin al’ummar Filato ya laƙume rayukan mutane 18

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Shugaban Ƙungiyar cigaba na ƙasa na al’ummar Irigwe a Jihar Filato ya gano waɗanda aka yi wa kisan gilla a daren Talata da ta gabata a ƙauyen Ancha ta masarautar Irigwe cikin ƙaramar hukumar Bassa na jihar.

Ƙungiyar ta bayyana cewar, mutane 18 ne suka rasa rayukan su a cikin farmakin na Irigwe da ya ɗauki tsawon lokaci na fiye da awowi biyu ana tabka shi.

Da yake bayar da ba’asin ƙididdiga akan farmakin, Sakataren ƙasa na ƙungiyar cigaban ta Irigwe, tare da wasu jami’an ƙungiyar, Davidson Malison, ya ce “yayin da wasu jama’a suke murnar shiga sabuwar shekara ta 2022, su kuwa jama’ar Rigwe sun shiga cikin sabuwar shekarar ce da rashin jin daɗi da takaici.

“Wannan ya alaƙa ne da wani hali, inda masu kasuwancin sharri suka samu cimma wani burin su na raya fulatanci da kuma share ƙabilar Rigwe daga doron ƙasa.

“Al’ummar Rigwe sun samu wani mummunan farmaki daga Fulani ‘yan ta’adda (kamar yadda waɗanda suka ƙetare rijiya da baya suka shaidar) a tsakiyar daren Talata, 11 ga watan Janairu na shekara ta 2022 a ƙauyen Ancha ta gundumar Miango, masarautar Rigwe ta ƙaramar hukumar Bassa.

“Farmakin, wanda ya shafe fiye da tsawon awanni biyu ba tare da wani katsalandan ko tsayar da shi ba, ya yi sanadiyyar kisan mutane 18 da raunana wasu mutane 6 yayin da aka ƙona gidaje guda 24 masu jimlar ɗakuna fiye da guda ɗari, haɗi da wasu kadarori na motoci, Babura da kayayyakin abinci da aka shigo da su daga gonaki duka an yi hasarar su, haɗi da sace-sacen dukiyoyi da warwason su.

“Abin baqin ciki da tashin hankali shine daga cikin waɗanda aka kashe, akwai jariri ɗan watanni uku wanda aka ƙone shi ƙurmus.”

Bisa bibiyar tarihin ta’addanci a yankin na Filato, “gabanin wannan farmaki na ƙauyen Ancha, an yi fashin mutane uku a ƙauyen Oureedam ta gundumar Kwall a daren bikin Kirishimati, inda aka kashe biyu daga cikin su yayin da na ukun ya samu raunuka daga harbin bindiga.

“Gabanin shiga wannan sabuwar shekara, a ranar 31/12/2021, an yi wa wasu mutane biyar farmaki a jikin dutsen hill, inda aka ƙone ɗaya har lahira, huɗu kuma suka samu raunuka.

“A ranar 7 ga wannan wata na Janairu, an yi wa wani ɗan shekara 49 mai suna Timeh Evi kwanton ɓauna tare da kashe shi a gonar sa ta noman rani da ke Nzhwerenvi, hatta gawar wanda aka kashe ba a same ta ba har ya zuwa wannan rana. Babur ɗinsa da injin bayin ruwa duka aka kwashe.

“Kazalika, a ranar 10 ga watan Janairu na wannan shekara ta 2022, an kai wa wani da matar sa farmaki a kuma ƙauyen na Ancha, yayin da mijin ya rasa ran sa, ita kuma matar ta samu raunuka, wanda a halin yanzu tana asibiti wajen jinya.

“Shugabancin na ƙungiyar cigaban Irigwe, sun ce kalmomin baki sun yi qarancin bayyana baƙin cikin su dangane da waɗannan halaye na rashin tausayi da yake samun al’ummar ta Irigwe.

“Mun yi kiraye-kiraye ga jami’an tsaro da gwamnati a lokatai masu yawa domin a samo hanyoyi na kawo ƙarshen waɗannan kashe-kashen rayuka akan jama’ar Rigwe, amma babu wasu matakai da aka ɗauka domin jin koke-koken mu, muna ƙara jaddada cewar, in dai muna cikin al’ummar Nijeriya kuma halattattun ‘ya’yan ta, muna kyautata sanya ran ganin ɗaukar ƙwararan matakai ba yaudara ba, kuzari ba kushe ba, kamun masu laifi ba bincike ba, da kuma adalci ba rashin adalci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *