Sabon Shugaban ƙaramar hukumar Doma ya yaba da zaɓukan bana

Daga JOHN  D. WADA a Lafiya

Bayan da aka kammala zaɓukan duka ƙananan hukumomin jihar Nasarawa, sabon shugaban ƙaramar hukumar Doma a jihar wanda aka zaɓa a inuwar jam’iyyar APC mai ci a jihar  Honorabul Jonathan Addra ya yi alƙawarin yin duka mai yuwa wajen kawo cigaba masu ma’ana a duka matakai a ƙaramar hukumar ta Doma bakiɗaya.

Honorabul Jonathan Addra ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu jim kaɗan bayan an rantsar da shi da sauran sabbin shugabannin duka ƙananan hukumomin jihar 13 wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar dake Lafiya babban birnin jihar a makon da ake ciki.

Ya ce ba shakka akwai alƙawura da dama da ya yi wa al’ummarsa a lokaci da yake yaƙin neman zaɓen nasa, saboda haka dole ne a yanzu da Allah ya ba shi nasara ya yi komai don tabbatar ya cika alƙawuran.

Sabon shugaban na ƙaramar hukumar Doma Honorabul Jonathan Addra ya kuma yi amfani da damar inda ya gode wa al’ummarsa na ƙaramar hukumar da suka fito ƙwansu da ƙwarƙwata suka zaɓe shi a lokacin kaɗa kuri’un inda ya tabbatar musu cewa ba zai ba su kunya ba.

Addra ya kuma yaba wa hukumar shirya zaɓuka na jihar dangane da gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin mafi inganci da tsari da kuma kwanciyar hankali kana ya buƙaci ta cigaba da hakan don cigaban dimukaraɗiyya.

Shi ma da yake bayyana wa wakilin mu ra’ayinsa game da zabin honorabul Jonathan Addra mataimakin gwamnan jihar ta Nasarawa dokta Emmanuel Akabe ya bayyana zabin Jonathan Addra a matsayin zaɓi nagari shiyasama al’ummar karamar hukumar ke cigaba da murnar nasararsa injishi tared a kira na musamman agareshi ya tabbatar yayi dafiya da kowa a shugabancin nasa.

A makon da ya gabata ne al’ummar jihar suka zaɓi sabbin shugabanninsu a duka ƙananan hukumomon jihar 13 daki-daki inda daga bisani kuma gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya rantsar da su a hukumance don kama aiki.