Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa da mataimakinsa sun ziyarci Buhari a Katsina

Daga BASHIR ISAH

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun bi Shugaba Buhari da shaidar lashe zaɓen da INEC ta miƙa musu har Daura don tayaurna da kuma sanya musu albarka.

Tinubu da Shettima sun wannan ziyarar ne bisa rakiyar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu.

Sauran ‘yan rakiyar sun haɗa da Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna), Atiku Bagudu (Kebbi), Dave Umahi (Ebonyi), Bello Matawalle (Zamfara), Abubakar Sani-Bello (Neja), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun), Badaru Abubakar (Jigawa) da kuma Simon Lalong (Filato).

Sabon zaɓaɓɓen shugaban ya yi amfani da wannan dama wanen nuna godiya ga Shugaba Buhari dangane da vouon bayan da ya ba shi yayin zaɓen da ya gabata.

Tare da kuma da miƙa masa shaida lashe zaɓen da Hukumar INEC ta miƙa masu a ranar Laraba don taya murna da sanya musu albarka.