Sabuwar cutar mashaƙo ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 61 a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI

Ɓarkewar sabuwar cutar mashaƙo wacce ake kira da diphtheria a turance ta kashe mutum 61 a jihar Kano.

An samu wannan rahoto a jihar Kano ranar 2 ga Maris, 2023.

Shugabar kes ɗin cutar ta jihar Kano, Dakta Salma Suwaid, ita ta bayyana haka a ranar Litinin a wani taro wanda Cibiyar dadaitawa da kariya ga cututtuka ta shirya.

Dakta Suwaid ta ƙara da cewa, jimillar marasa lafiya 783 ne yanzu haka suke kwance a asibiti. Inda 360 daga cikinsu mata ne, yayin da 423 daga ciki kuma maza ne.

Diphtheria matsananciyar cuta ce wacce nau’in ƙwayar cutar bakteriya mai suna Corynebacterium take haddasa ta. Takan kama hanci, maqogoro, wasu lokutan ma har fatar ɗan’adam.

Diphtheria tana da sauƙin yaɗuwa tsakanin mutane ta hanyar taɓawa kai-tsaye, da shafuwa da majinar marasa lafiyar ta hanyar tari, ko atishawa ko taɓa gurɓatattun kaya ko abubuwan marasa lafiyar.

Wannan ɓarkewar sabuwar cutar mashaƙon wacce take jawo mace-macen mutane da dama ba ta rasa nasaba da rashin yin rigakafi, da kuma rashin sinadarin warkar da cutar mai suna antitoxin a lokacin kamuwa da cutar.

A yanzu haka dai an tabbatar da ɓarkewar cutar a Jihohin Kano, Yobe, Lagos, Osun, da kuma Katsina.

Suwaid, wacce ita ma likitar ƙananan yara ce ta bayyana cewa, matsakaicin daɗewar da marasa lafiyar suke yi a asibiti shi ne kwanaki 4.

Sannan kuma ta ce sashen da aka ware don kula da marasa lafiyar an cika shi da kayan aiki da kuma isassun ma’aikata. Sannnan kuma ana ɗaukar matakan kariya ga ma’aikatan da ke asibitin.