Sabuwar Dokar Haraji: Ƙalubalen da ke gaban gwamnonin Arewa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun bayan da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da buƙatar kafa sabuwar Dokar Haraji, nake ta bibiyar muhawarar da ake tafkawa a kafafen watsa labarai, tsakanin ’yan siyasa, jami’an gwamnati da kuma masana tattalin arziki da sauran su. Ina jin babu wani batu da ya fi ɗaukar hankalin ’yan Nijeriya bayan batun cire tallafin man fetur, sai wannan sabuwar Dokar Haraji, da wasu ‘yan Nijeriya ke ganin alheri ce ga tattalin arzikin ƙasar nan, duba da tanade-tanaden da aka yi wa dokar. Amma da dama ‘yan Nijeriya, musamman ‘yan Arewa na kallon wannan doka a matsayin wata maƙarƙashiya da aka ƙullawa Arewa.

Waɗanda ke kan gaba wajen yaƙi da kafuwar wannan sauyin doka su ne Gwamnonin Arewa, da ke kallon babu wata masifa da ta tunkari arewacin ƙasar nan a ƙarƙashin mulkin Tinubu kamar wannan doka, wacce matuƙar ta samu karɓuwa to, jihohin Arewa ne za su fi ji a jikin su. Saboda kuwa kason kuɗaɗen raya ƙasa da suka saba karɓa daga Gwamnatin Tarayya, zai ragu sosai. Sakamakon yadda Arewa ke fuskantar komabaya a ɓangaren masana’antu da ƙere-ƙere, waɗanda a dalilinsu Arewa ba ta samun hanyoyin shigar kuɗaɗe masu yawa, ba kamar a jihohin kudu ba.

ɗaya daga cikin dalilan da suka janyo ’yan Nijeriya ke kuka da batun gyaran dokar harajin nan, akwai batun yanayin da aka shigo da batun, wato halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a ƙasar. Da dama jama’a na ganin wani ƙarin matsi za a shiga, domin kuwa dokar za ta iya ƙara tsadar farashin kayan masarufi da ma duk wani abu da talaka zai yi amfani da shi. Shin da gaske tsarin zai kawo wa tattalin arzikin Arewa komabayan kuma mai ya kamata shugabannin Arewa su yi? 

Binciken da na gudanar na gano cewa, gyaran da Gwamnatin Tarayya take so ta yi wa wannan dokar haraji ya zo ne ta fuskoki huɗu. Na farko, akwai Dokar Haraji ta 2024. Sai, Dokar Yadda Ake Gudanar da Harkokin Haraji. Dokar Kafa Hukumomin Karɓar Haraji, da kuma Dokar Haɗakar Hukumomin Karɓar Haraji. A manufar gwamnati, waɗannan dokoki za su taimaka ne wajen sauƙaƙa yadda ake biyan haraji da sarrafa shi. 

Misali, a Nijeriya ƙaramin ɗan kasuwa yana biyan haraji ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar da yake, da kuma harajin ƙaramar Hukumar da yake kasuwanci a ciki. A bisa sabon tsarin da ake so a kafa, za a riƙa biyan haraji ne a asusu guda ɗaya, don ya sauƙaƙa yadda biyan haraji zai yi wa ýan kasuwa sauƙi.

Dangane da harajin da ɗaiɗaikun mutane suke biya wanda a turance ake ce wa, Personal Income Taɗ (PIT), waɗanda ke samun abin da bai kai Naira dubu 800 ba, ba za su biya harajin komai ba, sai in ya zarta haka. Haka su ma masu kamfanoni, sabuwar dokar ta yi sassauci game da tsarin biyan harajin da suke yi na Companies Income Taɗ (CIT), inda a maimakon su biya haraji daga ribar da suka samu ta Naira miliyan 25, yanzu zai koma zuwa miliyan 50.

Sannan harwayau, dokar ta zo da tsarin haɗe dukkan ɓangarorin karɓa da tattara haraji na Gwamnatin Tarayya da na Jihohi, da kuma na ƙananan Hukumomi, inda kamar yadda na yi bayani a baya za a haɗe su waje ɗaya, in ya so daga baya sai a riƙa kasafinsa, gwargwadon abin da kowanne ɓangare ya tara. Don haka ne ma za a canja wa Hukumar Tattara Haraji ta ƙasa (FIRS) suna ta koma Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS). Game da batun yadda kasafin rabon harajin zai kasance kuwa, sabuwar dokar ta tanadi cewa, Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki kashi 10 cikin ɗari, sai Gwamnatin Jiha ta karɓi kashi 55 cikin ɗari, yayin da ƙaramar Hukuma za ta karɓi kashi 35 cikin ɗari.

To, fa! A nan ne inda tataɓurzar take. Domin kuwa Gwamnonin Arewa na ganin idan har wannan doka ta fara aiki, babu shakka za a durƙusar da jihohi ne, musamman waɗanda ba su da kamfanoni da masana’antun da za su riƙa biyan gwamnati da auki. Domin kuwa, in dai sai iya abin da ka zuba ne za ka kwasa to, kuwa jihohin Arewa ba za su samu wani kaso mai tsoka ba. Saɓanin tsohon tsarin da ake biyan kowacce jiha bisa kiyasin al’ummarta da gudunmawarta.

Wannan shi ya sa gwamnonin jihohin Kudu da al’ummar su ke ganin sabon tsarin ya zo musu a daidai, saboda suna da manya da matsakaita da ƙananan sana’o’i da dama, matatun man fetur, da teku inda ake shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, ba kamar a Arewa ba. Kuma dama sun daɗe suna ƙorafin cewa, abin da suka yi wahalar haɗawa na harajinsu ne ake bai wa Arewa. Don haka suke yi wa Arewa kallon cima-zaune. 

Ya zama dole a yi wa gwamnonin Arewa uzuri game da ƙorafin da suke yi, game da dokar haraji, wanda suke kallon ba ta yi musu adalci ba, duba da irin komabayan da jihohin su ke ciki. Babu shakka idan har ba gyara aka yi wa tsarin dokar ba, jihohi da dama ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba, ba za su iya gudanar da manyan ayyuka don cigaban jihohinsu ba. Sannan za a samu yawaitar karɓar bashi daga ƙasashen waje, ƙaruwar haraji ga talakawa.

Kamar yadda masana tattalin arziki ke ba da shawarwarin su na ƙwararru akan wannan matsala, lallai ya kamata Gwamnonin Arewa da masu ruwa da tsaki su ɓullo da hanyoyi na samun kuɗaɗen shiga a jihohin su, da rage dogaro da abin da suke samu daga Gwamnatin Tarayya, tunda yanzu alamu sun nuna cewa, ba zai yiwu su cigaba da samun yadda suke so ba. Lallai jihohin Arewa su ɓullo da wani tsari na bunƙasa harkokin kasuwanci a tsakanin su, samar da masana’antu da kamfanoni masu zaman kansu, da za su zuba jari, su samar da ayyukan yi, kuma su riƙa biyan haraji mai kauri ga gwamnati. 

’Yan Arewa masu ƙarfin tattalin arziki dake da manyan kamfanoni a kudancin ƙasar nan, su zo Arewa su buɗe kwatankwacin irin waɗancan masana’antun a jihohin su. Sannan jihohin Arewa masu ma’adinan ƙasa irinsu Bauchi, Kaduna, Filato, Zamfara, Taraba, Borno da sauran su, yanzu ne lokacin da za su mayar da hankalinsu wajen ganin sun mori albarkatun da Allah Ya hore musu, kamar su zinare, kuza, duwatsu masu daraja da man fetur, waɗanda yanzu su ne hankalin arzikin duniya ya karkata a kai. Lokacin da Arewa za ta riƙa nuna damuwa kan man fetur ya wuce, mu ma Allah Ya ba mu fiye da abin da suke yi mana alfahari a kai. 

Kamar yadda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya faɗa a jawabinsa na Sabuwar Shekara cewa, babu ja da baya ga batun sabuwar dokar haraji, saƙo ne gare mu ’yan Arewa cewa, zai yi wuya mu samu yadda muke so a wannan gwagwarmaya da muke yi ta yaƙi da kafuwar dokar. Ko da kuwa an yi wa dokar kwaskwarima, da wuya a koma yadda ake a baya. Don haka lallai ne tun yanzu mu san inda muka fuskanta. Mu dawo da hankalinmu gida don mu raya arzikin jihohinmu, mu zama masu iya dogaro da kanmu. Lallai ne canjin ba zai zo mana da sauƙi ba, amma idan muka jure za mu zo mu fahimci cewa, gara ma da haka ta faru!