Gaskiyar maganar ita ce sabuwar dokar haraji da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tura Majalisar Dokoki don amincewa ta tada ƙura. A zahiri hakan ya faru ne don dokar ta shafi rayuwar jama’a ne, jihohi da dukkan yankunan ƙasa. Abun nufi a nan in an duba harajin nan na musamman na fiton kaya ba kai tsaye ya shafi kowa ba ne kuma ba za a gane ko maida martani mai zafi ba don ya kan hau kan ‘yan kasuwa ne masu shigo da kaya daga ketare. Kazalika ba karɓar harajin ne kawai ya ja hankali ba yadda ya shafi raba shi ga jihohi bisa ga wa imma inda a ka tara harajin ko alakar jihar da waɗanda ke mallakar hajar da ta samar da harajin. Ina ganin ba don ƙungiyar gwamnonin arewa ta nuna rashin gamsuwa ga harajin ba da ma shawarar sake duba lamarin daga majalisar tattalin arziki da zai yi wuya bayanin ya dau hankali jama’a musamman ’yan arewa.
Hakanan yadda a ka yi ta alaƙanta lamarin da cewa zai kawo matsala ga rayuwar jama’a na jihohin da ba su da cibiyoyin tattalin arziki ya kara haddasa damuwa. Koma yaya mutum ya dau lamarin nan na haraji akwai buƙata ta kai tsaye ta bayani filla-filla daga gwamnatin Tarayya don fahimtar da ‘yan kasa cewa hakan ba shi da wata bahaguwar manufa. Ni abun da ma ya dame ni yanda fassarar ta nuna tamkar an kullawa yankin arewa gadar zare ne inda za a fifita yankin kudu ko ma kudu maso yamma. A kudu maso yamman ma a na batun jihar Leges. Wasu bayanai akwai karawa Borno dawaki a ciki kuma in ba an ɗau matakai ba za su ƙara farraka kan kasa ne a lokacin da a ke fatar haɗa kan ƙasar ta hanyar kawar da barazanar ’yan awaren Biyafara da masu rajin kafa ƙasar Oduduwa.
Talakawan talak na arewa sun riga sun saɓa da yanayin tsadar rayuwa kuma na tabbata ko da an aiwatar da harajin a yadda ya ke ba na ganin zai ƙara zafafa lamura fiye da yanda su ke yanzu. Wani lokacin tamkar talakawa na taya ’yan jari hujja faɗa ne kawai. Wasu jihohin ma ai ba a gane yadda gwamnoni ke yi da kuɗin da a ke turowa balle har wani ya tada hankalin sa kana bun da ba a damawa da shi. Sau da dama a kan turawa jihohi kuɗi don kula da rayuwa al’umma amma sai kaji shiru baa bun da a ka yi a kai. In sabon harajin na nufin raguwar kuɗi ga jihohin arewa ne to dama amfani na wa jama’ar wasu jihohin ke ci daga kuɗin da a ke turawa jihohin su? Tsaya tashar mota a jiha ka tambayi mutane ɗaya bayan daya Naira na wa a ka turawa jihohin su a wata, ina mai tabbatar ma ka z aka iya gajiya ba ka samu mai amsa tambayar ba.
Hatta yanda a ke samun harajin kayan masarufi wato ɓAT ba kowa ya ke lura da cewa ya na biyan harajin ba. A takaice ma abun da ya kara dago maganar a yankin arewa shi ne yanda a ka tafka muhawara gaban majalisar dattawa inda a ka ga mataimakin shugaban majalisar Barau Jibrin na jagorantar zaman da a ka lura ko fassara cewa na gurgunta yankin arewa ne. Hakanan a ka samu Sanata Ali Ndume na ƙalubalantar tsarin harajin. Daga nan sai wasu jagororin addini su ka yi sharhi kan lamarin da nuna rashin gamsuwa da harajin. Tun daga makon jiya wannan muhawara ta fara zafi da sukar wasu mutane da a ke ganin za a dau mataki a kan su a zabe mai zuwa. Duk abun da ya kamata a yi shi ne masana su duba dokar su kuma fahimtar da jama’a. Ya dace ma kowane gwamna a arewa ya shiga kafar yaɗa labaru na jihar sa ya yi bayani da amsa tambayoyin jama’a kan yadda lamarin ya ke. Cikin muhawarar da a ke yi tamkar ba wani gwamna a arewa in ba Babagana Umar Zulum na Borno ba.
Shin ko don ya fito ƙarara ya nuna rashin ribar dokar ne ko wani abu ne daban; gaskiya ya dace gwamnonin su fito su yi bayani indai akwai abun dauka a muhawarar. A yadda na fahimta wasu gwamnonin sun janye daga tada jijiyar wuya don wataƙila an sauya abun da ke damun su. Talaka dai ya sani akwai bambanci tsakanin sa da mai kuɗi hakanan jama’ar kasa gama-gari akwai bambanci tsakanin su da masu riƙe da madafun iko. Kafin mutum ya dau matsaya ya dace ya duba a wane ajin ya ke don gano irin riba ko akasin haka da matsayar sa za ta haifar. Tsorona kar mu riƙa riƙe takobin yaƙi a madadin wasu da ba su damu da mu ba ko idan daɗi ya samu ba sa tunawa da mu sai iyalan su kaɗai da sauran ‘yan amshin shata.
ƙasar nan na bukatar fahimtar juna da sauya tunani ne. in mun duba dokokin Nijeriya akwai ba wa kowa dama ya yi walwala ko addinin sa ba tare da tsangwama ba. Abun da ke kawo cikas a Nijeriya shi ne cusa bambancin rashin adalci bisa bambancin addini, ƙabilanci ko ɓangaranci. Masu sharhi na aza laifi kan ‘yan siyasa na amfani da logogin nan uku masu farraka kasa don cimma muradin su na darewa kan madafun iko. Da zarar sun hau madafun sai su jingine bambanci a zahiri don babu madogarar hakan a tsarin mulki. Wani abun takaici ma za ka ga wajen cin gajiyar Naira ba a nuna ko daya daga bambancin. In na fassara a kasari daga manyan ‘yan Nijeriya da zama ‘yan jari hujja ba na ganin zai rasa dalilan kare fassara ta.
Gamaiyar ƙungiyoyin arewa CNG ta buƙaci Majalisar Dokoki da gwamnatin Nijeriya su dakatar da sabon ƙudurin dokar haraji.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da shugaba Tinubu ya umurci ma’aikatar shari’a ta yi aiki tare da majalisa don tantance ƙorafe-ƙorafen jama’a kan ƙudurin.
A taron nazartar sabon ƙudurin, ƙungiyar ta ce akwai ƙarancin bayani da kuma gaggawa wajen neman amincewa da ƙudurin.
Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar Nastura Ashir Sharif ya ce haƙiƙa jama’ar arewa ba sa marawa ƙudurin baya “abun da mu ke gani shi ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da wannan abu a majalisa ta janye shi, a dawo a zauna da gwamanoni da ƙananan hukumomi da masana, kowa ya kalli abun nan ya karanta sh dalla-dalla kowa ya kawo ra’ayin sa da gyaran da ya ke so a yi”
Shi kuma tsohon minista a ma’aikatar kuɗi Dokta Yarima Lawan Ngama ya ce ya duba ƙudurin inda ya ce da alamun gwamnati ta yi bitar sa daga bisani ta hanyar mika haraji ga jihar da a ka yi amfani da haja ba inda a ka samar da ita ba duk da hakan bai shiga rubutun a hukumance ba “mutane su kwantar da hankalinsu, da farko ba haka a ka shiryo ba. Da zafi ya yi zafi sai a ka yi kwana kuma kwanar ta yi ma na kyau a Nijeriya gaba ɗaya ba maganar arewa kaɗai ba”
Mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan siyasa Ibrahim Kabir Masari ya ce kofofin shugaban a buɗe su ke ga duk ƙorafin da jama’a za su gabatar ”shi shuagban ƙasa mai sauraron mutane ne matsalar mutane ita ce damuwar shi a shirye ya ke ya ajiye ta shi fahimtar ko ra’ayin shi tun da mulki a ke yi na dimokraɗiyya”
Yanzu dai za a fahimci cewa gwamnati na kan bakan ta na samun amincewa da ƙudurin amma bayan kawar da wasu sassa da jama’a ba za su lamunta ba.
Shugaba Tinubu ya umurci ma’aikatar shari’a ta yi aiki da majalisa wajen daidaita dokar haraji:
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ba wa ma’aikatar shari’a umurnin yin aiki tare da Majalisar Dokoki don daidaita sabuwar dokar haraji kafin amincewa da ita.
Ministan labaru Muhammad Idris ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar kan saƙon shugaban.
A nan shugaban ya umurci waɗanda su ka tsara ƙudurin su zauna da majalisa don gano abubuwan da su ka daurewa jama’a kai don samar da maslaha.
Kasancewar lamarin na neman kawo baraka tsakanin sashin kudu da arewacin Nijeriya, zai zama mai muhimmanci ma’aikatar shari’ar ta sake yi wa dokar bita don samun karɓuwa ta bai ɗaya yadda wani yanki ba zai cutu ba.
Kammalawa;
Majalisa dai za ta gana da tawagar sashen zartarwa kan wannan ƙudurin doka. A na tsammanin za a yi la’akari da muradun duk sassan ƙasa wajen bitar ƙudurin in ma ba za a iya jingine shi gaba ɗaya ba. Duk wani tsari da zai fifita wani yanki kan wani a Nijeriya ba zai dace da yanayin ƙasar mai ƙabilu da addinai daban-daban ba. Nijeriya na buƙatar matakai ne na bai daya daga gwamnatin tsakiya don kare kambin kirarin ƙasar na kasancewa ƘASA ƊAYA AL’UMMA ƊAYA. Har dai a na son ƙasar ta magance fitinar rabuwar kawuna sai Gwamnatin Tarayya ta kaucewa bijiro da duk wani tsari da zai samu fassarar harshen damo.