Sabuwar manufar Amurka kan Sin ba ta canja tunaninta na yakin cacar baka da fin ƙarfi ba

Daga CMG HAUSA

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya gabatar da wani jawabi game da manufar ƙasarsa kan ƙasar Sin a jami’ar George Washington a ranar 26 ga wata, inda ya bayyana cewa, Amurka tana aiwatar da manufar “zuba jari da hada kai da yin takara” kan ƙasar Sin, amma kafin hakan, ya taba bayyana cewa, manufar ita ce:

“takara da haɗin gwiwa da nuna ƙiyayya”. Duk da cewa, akwai bambanci kaɗan tsakaninsu, ainihin yanayin da Amurka ke ciki shi ne, ta gamu da cikas yayin da take matsawa ƙasar Sin lamba. Amurka ba ta sauya tunaninta na yakin cacar baka da nuna fin ƙarfi ba, sai dai sauya dabarunta na hana ci gaban ƙasar Sin kaɗai.

A cikin jawabinsa, Blinken ya sake yada ƙarairayin wai kasar Sin tana kawo wa tsarin ƙasa da ƙasa babban ƙalubale mai ɗorewa. Hakika wadda ke kawo wa tsarin ƙasa da ƙasa ƙalubale mai tsanani ita ce Amurka.

Ga misali, kai wa Iraki hari, da tayar da yaƙin basasa a Libya da Syria, da ficewa daga yarjejeniyar makaman nukiliya ta Iran, da ɓarkewar rikicin Ukraine, sakamakon sa ƙaimi kan Nato ta fadada zuwa gabashi, da kitsa ƙiyayya tsakanin kasa da kasa. Duk waɗannan sun nuna cewa, Amurka ce ke zaman ƙalubale mafi girma ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasashen duniya.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa