Sadarwa: Gwamnati ta tsawaita wa’adin shirin haɗe layukan sadarwa da lambar NIN

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa’adin shirin haɗe Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa da layukan sadarwa da makonni 8 domin bai wa ‘yan ƙasa isasshen lokaci don su sada layukan sadarwarsu da lambar NIN.

Sabon wa’adin da gwamnatin ta tsayar yanzu, shi ne zuwa ranar 6 ga Afrilu mai zuwa.

Daraktan Hulɗa da Jama’a na Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, Dr Ikechukwu Adinde, shi ne ya ba da bayanin haka a ranar Talata. Inda ya ce, Ministan Sadarwa Isa Pantami ne ya ba da umarnin tsawaita wa’adin bayan taron kwamitin sanya ido kan shirin haɗe lambar NIN da layukana sadarwa.

Pantami ya ce, an ƙara wa’adin ne domin bai wa ‘yan Nijeriya da kuma baƙin da aka halasta musu zaman ƙasa ƙarin lokacin da zai bai wa kowa damar haɗe layinsa na sadarwa da lambar shaidar ɗan kasa.

A cewarsa, “Rahoto ya nuna cewa lambar NIN milyan 56.18 ne suka shiga hannun kamfanonin sadarwa. Sannan an tarar da kowace lamba na ɗauke da bayanan layukan sadarwa 3 zuwa 4.”

Ya ci gaba da cewa, “Wannan adadi da aka samu ya nuna an samu ci gaba mai ma’ana game da shirin, idan aka kwatanta da adadin milyan 47.8 da kwamitin ya ruwaito an samu a ranar 18 ga Janairun da ya gabata.”

Ministan ya ƙara da cewa, cibiyoyin yin rijistar Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa sama da 1,060 ne aka samar a faɗin ƙasa don amfanin jama’a.

Idan dai ba a manta ba, ranar 9 ga Fabrairun da ake ciki ne gwamnati ta soma tsayarwa a matsayin ranar da za a soma rufe layukan da ba a haɗe su da lamabar NIN ba a faɗin kasa, sai ga shi ta tsawaita wa’adin shirin ya zuwa 6 Afrilu mai zuwa.

Pantami ya yi amfani da wanan dama wajen miƙa godiyarsa ga hukumomin gwamnati da ma masu zaman kansu da suke ba da gudunmawarsu wajen gudanar da shirin yin rijistar.