Safarar sassan mutum: Kotu ta ɗage shari’ar Ekweremadu zuwa Oktoba

Daga BASHIR ISAH

Kotun Turai ta ɗage ci gaba da shari’ar tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ike Ekweremadu, zuwa 31 ga Oktoban 2022.

Rahotanni daga kasar sun ce, ɗage shari’ar na nufin za a ci gaba da tsare Ekweremadu din a gidan yari har zuwa ranar da aka tsayar don ci gaba da shari’ar.

Sai dai kotun ta bada belin Beatrice.

Ana tuhumar Ekweremadu da matarsa Beatrice ne kan safarar sassan mutum.