Daga USMAN KAROFI
Mai baiwa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Shawara na musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kai, Sunday Dare, ya buƙaci jama’a su ƙara hakuri dangane da ƙorafe-ƙorafe da ake yi kan sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa a yanzu.
Ya bayyana cewa shugaban ƙasa yana aiki tuƙuru domin al’ummar Nijeriya su amfana daga ƙudurorinsa na tattalin arziki, kuma ya cancanci yabo bisa irin ayyukan da ya ke yi. Dare ya jaddada cewa Tinubu ya sha wahala sosai wajen kawo canji ga al’umma, inda yake kwanciya da asuba bayan ya gudanar da ayyukan ƙasa.
Tun lokacin da aka rantsar da Tinubu, ya bayyana ƙarshen tallafin man fetur tare da amincewa da bada damar faɗuwar darajar Naira. Waɗannan matakan, tare da wasu canje-canje na haraji, sun haifar da tashin farashin kayan abinci da sauran kayayyaki. Duk da haka, Dare ya ce ya dace a yaba masa maimakon sukar lamuransa na tattalin arziki.
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television, Dare ya ce, “Kasancewar akwai masu cin moriyar tallafin man fetur da suka jima suna samun biliyoyin Naira, ya dace a yaba wa Tinubu kan juriya da ƙwazo wajen kawo ƙarshen tsarin. Wannan abu ne da shugabannin baya suka kasa yi, amma ya dace a yaba masa,” inji shi.
Dare, wanda tsohon minista ne na wasanni da ci gaban matasa, ya ƙara da cewa Tinubu mutum ne mai ƙwarewa a sha’anin mulki, wanda ke gudanar da ayyukansa cikin tsanaki da himma. Ya ce ya yi aiki tare da shugaban ƙasa na tsawon shekaru bakwai, kuma yana iya tabbatar da cewa Tinubu mutum ne mai sadaukar da kansa, wanda ke kwanciya bayan kammala aiki da asuba, domin biyan buƙatun al’ummar Najeriya.