Sai gwamnati da gidajen jaridu sun haɗa kai wajen ciyar da Nijeriya gaba – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira da a ƙarfafa alaƙa tsakani gwamanti da gidajen jaridu wajen sauƙe nauyin harkokin ci-gaba a Nijeriya.

Shettima ya faɗi hakan ne a ranar Talata, a lokacin da jagororin ƙungiyar editocin Nijeriya ta Nigeria Guild of Editors da suka kai masa ziyara Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ya na mai nuna muhimmancin taimakon gwamnatin a harkokinsu.

Ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a ce an fifita shugabanci sama da siyasa don haka a haɗe kai da gidajen jaridu.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tsokaci game da ƙalubalen tattalin arziƙi da ke shafar harkar jarida, ya na mai kira ga gwamnatin da ta taimaka wa ɓangaren don samun inganci.

Kashim ya kuma yi kira ga editocin su ke tabbatar da adalci yayin ayyukansu na jarida don cigaba da riƙe martabarsu.

A lokacin da ya ke magana yayin ganawar, shugaban ƙungiyar, Mista Eze Anaba na jaridar Vanguard ya yaba wa mataimakin shugaban ƙasar a ƙoƙarinsa na bayyana ayyukan da gwamnati ke yi na farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa ga al’umma bisa yadda ya dace.

Ya kuma bada tabbacin cewa, a shirye gidajen jaridu suke su haɗe kai da gwamnati.