Sai Gwamnatin Buhari ta sauka ‘yan Nijeriya za su riƙa yaba ayyukanmu – Sanata Lawan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewa, mafi yawan ’yan Nijeriya na kwana da tashi cikin farin ciki da su ’yan majalisa. Wannan farin cikin kuwa, jin daɗi ne da su ke yi ga mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce, sai ma bayan sun kammala wa’adin mulkinsu ne akasarin ‘yan Nijeriya za su riƙa santin rubutawa da furta kalaman alheri kan Majalisar Dattawa da ta Wakilai da ma Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, dangane da ɗimbin nasarorin da suka samar.

Lawan ya yi wannan bayani ne a wurin wani taron taya shi murnar cika shekaru 63 a duniya, wanda aka shirya a ranar Laraba, a Abuja.

Wannan kalami na Sanata Lawan ya zo daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke kushe ‘yan majalisa, su na zargin cewa ba su komai wajen taka wa ɓangaren shugaban ƙasa da ministoci da sauran ma’aikatu burki.

Sannan kuma ana jin haushin majalisar tarayya da ta dokoki cewa duk abin da shugaban ƙasa ya kai masu, sai su sa hannun amincewa ido-rufe.

Musamman an fi damuwa da irin yadda su ke amincewa da tulin bashin da Buhari ke ciwowa, wanda ba su tsayawa su duba makomar Nijeriya nan gaba, sai kawai su amince Buhari ya riƙa kinkimo bashi daga waje.

Ana kuma jin haushin Majalisar Dattawa da bin son zuciyar su, ba ƙaƙƙautawa ga ‘yan Nijeriya, waɗanda su ka zaɓe su ba.

An sha kiran ‘yan Majalisa a ƙarƙashin Sanata Ahmad Lawan ‘yan amshin Shata, ba kamar ta lokacin Sanata Bukola Saraki ba, wadda ake kira bangon tama.

Lawan da kan sa ya taɓa cewa bai damu don ana kiran su ‘yan amshin Shata ba, matsawar dai ya yi amanna cewa duk abin da za su amince a yi, to abu ne da zai amfani jama’a.

“Wata rana bayan mun sauka, masu kiran mu ‘yan-amshin-Shata sai sun riƙa furta kalaman yabo da rubuta ɗimbin alkahiran da mu ka yi na cigaban al’umma baki ɗaya.

“Akasarin ‘yan Nijeriya na farin ciki da abin da mu ke aikatawa. Ban ce ba mu yin kuskure ba, mu na yin kuskure tabbas, amma kuma mu na yin gaggawar ganin cewa mun gyara kura-kuran.”

Da ya ke magana kan matsalar tsaro, Lawan ya ce ‘yan Nijeriya sun gaji da labaran yawan kashe-kashen da ake yi a ƙasar nan. Yayata yawan waɗanda ake kashewa ba abin alheri ba ne ga ƙasar nan.”

Sai dai kuma ya nuna cewa duk da gaggauta amincewa a ciwo bashi da su ke wa Shugaba Buhari, su ma sun damu sosai da yawan bashin da ake ciwowa.

Ya ce a haka za a ci gaba da ciwo basussuka, matsawar hukumomin da tara kuɗaɗen haraji ke wuyan su ba su tashi tsaye sun riƙa tara wa gwamnati haraji mai tarin yawa ba.

“Babu mai so ya riqa ɗirka wa kansa tulin bashi, ko da ƙasa, kamfani ko mutum ne shi kaɗai ko iyalin sa. Amma idan babu hanyoyin da kuɗi za su shigo, to fa babu tsimi, babu dabara sai an riƙa ciwo bashi,” inji Lawan.