Sai kun riƙa biyan Dala 300 – Gwamnatin Tarayya ga masu helikwafta

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Nijeriya (NAMA) ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara karɓar Dala 300 daga masu amfani da jiragen helikwafta a matsayin kuɗin sauka.

Daraktan gudanar da Hanyoyin Samaniya na hukumar, Mista Taiwo John ya bayyana hakan a Kano, yayin taron ƙungiyar masu kula da hanyoyin sama (NATCA) karo na 53 wanda ake yi duk shekara, ya na mai cewa tarar za ta rage wa hukumar nauyin barazanar kuɗi da ta ke fuskanta.

Da farko dai sun fara karɓar tarar daga masu helikwafta inda gwamnati ta buƙaci su dakata saboda waɗansu dalilai, inda a yanzu kuma ya ce za su dawo da karɓa nan da mako guda.

Gwamnatin Tarayya ta Ma’aikatar Sufurin Jiragen sama ta samar da tsarin NAEBI da zai riƙa karɓar kuɗaɗen sauka da kuma tashin helikwafta daga wuraren albarkatun mai da kuma masu amfani da na gida.