Sai mun sha wuya muke lodi a matatar Ɗangote – IPMAN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta ƙasa, IPMAN, ta ce mambobinta ba sa samun loda fetur a matate man fetur ta Dangote duk da cewa sun biya naira biliyan 40 ga kamfanin NNPCL.

Shugaban IPMAN, Abubakar Garima ne bayyana haka a tashar Channels cikin shirin Kasuwanci, inda ya ce sun yi mamaki da suka ji Dangote yana cewa dillalan man fetur ba sa zuwa matatarsa sayen mai.

“Idan zai sayar da mai kai-tsaye, za mu saya saboda dole sai mun biya, za a ba mu man. Yanzu haka akwai kuɗinmu naira biliyan 40 a wajen NNPCL, amma ba ma samun kayan. Kwanan nan wasu mambobinmu da NNPCL ta tura matatar Dangote, inda motocinsu suka kwashe kwana huɗu a can ba tare da sun samu man ba.”

A ranar Talata ce dai Alhaji Aliko Dangote ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya bayyana wa manema labarai bayan ganawar cewa yana litar mai sama da miliyan 500 a ajiye, amma dillalan man ba sa sayen fetur ɗin.

A ƙarshe, shugaban IPMAN, ya yi kira ga Dangote da ya duba farashin man matatarsa, sannan ya kwatanta da farashin man na ƙasashen waje.