Sai nan da 2025 za a kuɓutar da ‘yan Nijeriya miliyan 25 daga ƙangin talauci – Osinbajo

Daga Amina Yusuf Ali

Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, Nijeriya ta gama tanadinta tun daga wannan shekarar ta 2021 domin tabbatar da cewa an kuɓutar da ‘yan Nijeriya mutum miliyan 25 daga ƙangin talauci sannan kuma za a kange wasu miliyan goma daga afkawa ƙangin talaucin.

Osinbajo wanda Sakataren Gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ya wakilta ne ya bayyana hakan a taron tattalin arziki wanda NiDCOM ta shirya. Inda ya ƙara da cewa, tallalin arzikin Nijeriya ya ƙara bunƙasa a yanzu.

Sannan kuma sanadiyyar sabbin abokan hulɗar da Nijeriya ta ƙara samu sakamakon annobar Covid19, za a samu masu zuba jari sosai a tattalin arzikin ƙasar daga hulɗarta na ƙasashen ƙetare.

Shi dai wannan taron tattalin arziki na NDIS, NiDCOM tana shirya shi kowacce shekara. Kuma wannan shi ne karo na uku.