Saka murmushi a fuskar mabuƙata ke ba ni ƙwarin gwiwa – Maryam Yaro

“Babban burina shine inganta rayuwar al’ummar Zamfara da sana’o’i”

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna

A kullum iyaye mata ba su bari a bar su a baya, musamman a wannan zamanin su ne sahun gaba wurin taimakon al’umma a kowane yanki. Hajiya Maryam Shehu Yaro (Zarar Maru) ’yar asalin Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara ita ce mace ta farko da aka ba wa sarautar Zarar Maru a masarautar Maru da ke Ƙaramar Hukumar Muru, Jihar Zamfara. Allah Ya albakarkaci Hajiya Maryam da ‘ya’ya biyu mata, Hauwa da Amira. Hajiya Maryam gogaggiyar ‘yar boko ce, kuma ta na da ilimin addini, wadda kusan dukkan karatun ta a qasahen waje ta yi, kuma ta yi ayyuka a manyan ma’aikatun gwamnati daban-daban a ƙasar nan. Wasu daga cikin inda ta yi aiki sun haɗa da Shevron, Oil And Gas, National Pension Commission da sauran su. Zarar Maru mace ce da ta duƙufa wurin aikin taimako ga mutanen yankin ta na ƙaramar hukumar Maru da sauran al’ummar Jihar Zamfara. Wanda a kullum ka ziyarci gidan ta da ke Abuja za ka tarar da jama’a cike daga Jihar Zamfara maza da mata. Wasu daga cikin aikin taimakon da ta ke yi su ne; Bada taimako ga marayu, gajiyayyu, marasa ƙarfi, bada gudunmawa wurin yin karatu da sauran ayyukan agaji ga al’umma. Duk da cewa a Abuja ta ke zaune, amma bai hana ta yin wani hoɓasa ba wurin taimakon al’ummar ta.  Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Muhammad, ya zanta da Hajiya Maryam Yaro game da muhimman abubuwa kamar rayuwar ta, irin taimakon da ta ke yi wa al’umma, kyautar karramawa da gidauniyar ‘Rising Star’ su ka yi mata da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

MANAHAJA: Hajiya za mu so mu ji wace ce Hajiya Maryam?
MARYAM: Kamar yadda aka sani suna na Maryam Shehu Yaro, daga family ɗin Alhaji Haje, an haife ni a daular Zazzau a farko-farkon 1970, na yi dukkan karatu na a ƙasashen waje da nan gida Nijeriya. Mu ne sahun farko a Jami’ar Abuja. Na yi ayyuka da ma’aikatun gwamnati da dama.

Ran ki ya daɗe kin hau karagar mulki a matsayin Zarar Maru ta farko  a Jihar Zamfara, wani irin ƙalubale ki ka fuskanta?
Gaskiya ƙalubalen da mu ke fuskanta rashin tsaron nan ne da kuma tashin hankali da mu ke fama da shi a Jihar Zamfara. 

Yadda cibiyoyin gargajiya su ke gudanar da harkokin su mabanmbanta daga nan zuwa can, za mu iya sanin asalin tarihin sarautar ki ta Zarar Maru?
Gaskiya wannan sarauta ya zo ne daga ayyukan da iyaye su ka bari ne. Ka ga sarki ya amince, kuma bai so sunan su ya vace ba, dalili ɗiya farko ta family, sai aka ba ni Zarar Maru, ma’ana Tauraruwar Maru.

Hajiya yaya ki ke gudanar da harkokin wannan sarauta ta ki?
Saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a Jihar Zamfara, gaskiya mu na samun yin taro a nan Abuja. Mukan ɗan haɗu a nan Abuja da wasu ƙungiyoyin mata mu shirya abubuwan da za a iya yi wa marayu, waɗanda mazajen su suka mutu da matasa mu harhaɗa, abin da mu ka yi a nan sai mu tura masu, kuma lokaci zuwa lokaci na kan ɗan leƙa. 

Hajiya ki na ɗaya daga cikin waɗanda su ka samu damar lashe kambin karramawa na ƙungiyar ‘Rising Star’, ya ki ka ji a ran ki?
Gaskiya na yi matuƙar murna da wannan karramawa da gidauniyar ‘Rising Star’ su ka yi mani, kuma zan yi amfani da shi don ganin na ƙarfafa wa na ƙasa don su ma yi abin kirki. Allah ya yi mana jagora.

A lokacin da aka tuntuɓe ki aka sanar da ke cewa ki na ɗaya daga cikin waɗanda ki ka lashe gasar ya ki ka ji?
(Dariya), gaskiya sai da na ji shock, don ban yi tsammani ba, irin daga ina ɗin nan, sai da aka tura mani hoton kambun ta waya, na yi ihu na ce da gaske ne.

Me wannan karramwa za ta ƙara miki game da ayyukan ki ko kuma rayuwar ki?
Gaskiya zai ƙara buɗe mani ido na. Dukkan abin da ka ke yi na alheri duk ƙanƙantar shi, kada ka yi tunanin ba a gani, domin idon mutane na kai, su na ganin abin da ka ke yi. Don haka ka yi ƙoƙari ka yi abu mai kyau yadda za ka iya yi daidai ƙarfin ka.

Wani irin tallafi Zarar Maru ta ke yi wa jama’ar ta na Maru, musamman masu ƙaramin ƙarfi?
Gaskiya ina aika gudunmawa ta gare su lokaci zuwa lokaci, ko yanzu ina yin abubuwan da su ka kamata.

Hajiya mene ne mataki na gaba a rayuwar ki?
E to, tunda ga shi gidauniyar ‘Rising Star’ sun ga irin abubuwan da na ke yi, har suka karrama ni, masarautar Maru ma kuma sun ba ni sarauta, komai ya na tafiya yadda ya kamata, ga kuma taimakawa mutane.

Ya ki ke kallon kan ki nan da shekara goma?
A shekara goma nan gaba? Babban buri na in inganta rayuwar al’umma da sana’o’i a faɗin Jihar Zamfara, zan buɗe ‘Focational Centres’, a Jihar, wannan abu ne da na ke so na yi, in tallafawa matasa da sana’a’o’i iya ƙarfi na, ka san duk sanda ka saka wa wani murmushi a fuskar sa, za ka ga  mutum na cigaba a rayuwa, kai ma za ka cigaba, ba maganar kuɗi ba ne, maganar cigaba ne da ƙarfafa wa mutum don samun cigaba.

Me ya ke baki ƙwarin gwiwa a kan ayyukan alkhairi da ku ke yi, kuma wa za ki gode wa?
Saka wa mutune murmushi a fuskar su, zai baka ƙwarin gwiwa. Da farko ina yi wa Allah godiya a kan komai, iyaye na da su ka rasu, wanda su ka ɗauki nauyin ilimi na, dole in yi godiya a gare su, sai kuma ɗan’uwa na Al-Imash da ya ke  ba ni gudunmawa a kan sarauta ta ta Zarar Maru, na gode sosai, sai ƙanena Yusuf shi ma yana tare da ni a kodayaushe, sai kuma dangina.

Hajiya Maryam tare da ‘ya’yanta da ‘yan uwa

Su wane ne waɗanda su ka fi kusanci da ke a cikin al’umma? 
Bari in faɗi abin da Baban mu ya koya mana. Ni ta kowa ce, kuma ni ba ta kowa ba ce.

A matsayin ki ta uwa mai jagorantar al’umma, me za ki cewa iyayen da ba su bari ‘ya’yan su mata su yi karatun boko ko kuma mazan da ba su bari matan su su yi aikin gwamnati da sauran ayyuka?
Kowa dai a yanzu ya san cewa mata su ne ƙashin bayan al’umma na duniya baki ɗaya, ilimin su ya na da muhimmanci matuƙa, mu fara da wannan ba ma aiki ba tukun. A bar su su je makaranta saboda su ƙaru da ilimin da su ma za su iya koyawa ‘ya’yan su, domin su ta shi saboda su zama mutanen ƙwarai.

Ko ki na da saƙo ga gidauniyar ‘Rising star’?
Ina yi masu fatan mafifincin alkhairi.

Godiya ta musamman?
Gaskiya godiya ta na kan ‘Rising Star’ ne da suka karrama ni. Ina godiya sosai da wannan gagarumar kyauta. 

Hajiya mun gode.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *