Sakamakon Zaɓe: Gawuna ya sha gaban Abba a Kano

Daga BASHIR ISAH

Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnoni da ya gudana ranar Asabar, a halin da ake ciki bayana sun ce ɗan takarar Gwamna na APC a Jihar Kano, Nasir Gawuna, ya sha gaban abokin hamayyarsa na NNPP, Abba Kabiru Yusuf da yawan ƙuri’u.

Da fari Yusuf ne ke kan gaba da yawan ƙuri’u amma daga bisani lamarin ya juya kan Gawuna.

Kawo yanzu dai INEC ta bayyana sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomi 14 a cibiyar tattara sakamakon zaɓen.

Ƙananan hukumomin su ne: Rano, Rogo, Makoda, Kunchi, Wudil, Karaye, Tsanyawa, Minjibir, Gabasawa, Ajingi, Bagwai, Kabo, Shanini da kuma Albasu.

Daga sakamakon da hukumar zabe ta bayyana, APC na da ƙuri’u 237,146 yayin da NNPP ta samu ƙuri’u 235,956, wato bambamcin ƙuri’u 1,190 ke nan ke tsakaninsu.

Ga ƙarin bayani game da sakamakon zaɓen:

RANO

DP – 80
APC – 17,090
NNPP – 18,040
PDP – 225
PRP – 10

ROGO

APC – 11,112
ADP – 42
NNPP – 18,559
PDP – 124

MAKOƊA
APC – 15,006
ADP – 83
NNPP – 13,956
PDP – 101

KUNCHI
APC – 13,215
ADP – 62
NNPP – 10,674
PDP – 39

WUDIL
APC – 20,299
ADP – 276
NNPP – 21,740
PDP – 118

KARAYE
APC – 14,515
ADP – 63
NNPP – 15,838
PDP – 77

TSANYAWA
APC – 18,746
ADP – 78
NNPP – 16,769
PDP – 71

MINJIBIR
APC – 16,039
ADP – 148
NNPP – 17,575
PDP – 189

ALBASU
APC – 16,959
ADP – 55
NNPP – 19,952
PDP – 293

GABASAWA
APC – 17,584
ADP – 91
NNPP – 19,507
PDP – 1,269

AJINGI
APC – 14,438
ADP – 306
NNPP – 15,422
PDP – 103

KABO
APC – 23,599
ADP – 149
NNPP – 16,963
PDP – 2,118

BAGWAI
APC – 21,295
ADP – 88
NNPP – 17,311
PDP – 51

SHANONO
APC – 17,249
ADP – 66
NNPP – 13,650
PDP – 272