Sakamakon zaɓen gwamna daga ƙananan hukumomin Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sakamakon zaɓen gwamna ya fara fitowa daga Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Sakamakon ya nuna cewa, jam’iyyar PDP ne ke kan gaba duba da ƙananan hukumomi uku da INEC ta gabatar.

Ya zuwa yanzu, PDP ce ke da mafi yawan ƙuri’u daga sakamakon zaɓen da ya shigo hannun majiya.

A ɓangare guda, jam’iyyar PDP ta zargi APC da ƙoƙarin yiwa jami’an zaɓe barazana a wasu ƙananan hukumomin jihar.

A cewar PDP, dukkan sakamakon zaɓen da aka ɗaura a kafar yanar gizo sun nuna PDP ce ya yiwa APC cin kaca.

Wannan zargi na PDP dai na fitowa ne daga wata sarnarwar da aka a fitar a Gusau a ofishin hadimin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar.

Ya bayyana cewa, alamu sun nuna gwamnatin jihar mai ci bata ji daɗin yadda sakamakon zaɓen ke fitowa da nasarar PDP ba.

Ƙaramar hukumar Anka:

APC – 10,156
PDP – 17,116

Ƙaramar hukumar Bukuyum:

APC – 10,321
PDP – 24,341

Ƙaramar hukumar Zurmi:

APC – 21,027
PDP – 24,328