Sakataren MOPPAN ya zama jami’in shirye-shiryen Kamfanin Northflix

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An farkon makon nan aka naɗa fitaccen jarumin Kannywood, Umar Gombe, a matsayin jami’in shirye-shirye na Kamfanin nuna finafinai na Northflix.

A cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun Shugaban Kamfanin Northflix, Alhaji Jamilu Abdulsalam, ta nuna cewa, an naɗa Mataimakin Sakataren MOPPAN na Ƙasa, wato Umar Gombe, a matsayin Jami’in Shirye-shiryen kamfanin na farko.
Gombe zai jagoranci fannin shirye-shirye na kamfanin wajen bunƙasa harkar kasuwancin finafinan Hausa a duniya. 

A yayin da ya ke yin ƙarin haske dangane da kamfanin, Alhaji Abdulsalam ya nuna cewa, musabbabin buɗe cibiyar Northflix shi ne, domin ƙara haska finafinan Kannywood a idon duniya ta hanyar kasuwanci, wanda a cewarsa, tuni duniya ta koma yanar gizo wajen sarrafa harkokin kasuwanci, musamman ma na finafinai.

A cewarsa dai, kamfaninsa ya sami haɗin gwiwa da wasu kamfanonin shirya finafinai na Kannywood, waɗanda suka haɗa da FKD Productions, Saira Movies, Dorayi Movies, Uzee Concept, Maishadda Movies da sauransu. 

Takardar dai ta nuna cewa, ana sa ran Gombe zai yi amfani da ƙwarewarsa wajen tafiyar da ayyukan da aka ɗora masa.

Shi ma Kakakin MOPPAN na Ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya tabbatar da wannan naɗi a wata sanarwa da MOPPAN ƙarƙashin jagorancin, Alhaji Ahmad Muhammad Sarari, ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakinta na ƙasa.