Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani fitaccen matashin jam’iyyar APC, Kuma mataimaki na musamman ga jamil’iyyar APC ta Ƙasa kan tsare tsare, Kabiru Oro Ƙaura Namoda, ya yaba wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa sake naɗa Fatima Umaru Aliyu Shinkafi a matsayin babbar sakatariyar hukumar bunƙasa ma’adinai. Yana mai bayyana cewar naɗin ya cancanta.
Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sake naɗa Hajiya Fatima Umaru Shinkafi a matsayin babbar sakatariyar asusun bunkasa ma’adanai PAGMI.
Kabiru Oro Ƙaura Namoda a wata sanarwa da ya fitar yace Hajiya Fatima Umaru Aliyu Shinkafi ta nuna jajircewar ta ga ajandar sabunta fata na shugaban ƙasa Bola Tinubu.
“Mu ’yan asalin Ƙaura Namoda masu goyon bayan APC a Abuja mun yaba da ƙoƙarin Hajiya Fatima Umaru Aliyu Shinkafi da goyon bayan da muke baiwa Shugaba Tinubu da gwamnatin sa, kuma shine babban abin da muka sa a gaba”.
“Mun godewa shugaban ƙasa Tinubu kan wannan karimcin tare da ba shi tabbacin ci gaba da goyon bayan mazaɓar Fatima Umaru Aliyu Shinkafi da gwamnatin sa”.
Kabiru Oro ya ci gaba da cewa, Hajiya Fatima Umaru Aliyu Shinkafi ta tashi tsaye wajen tallafawa al’ummar mazaɓarta da Jihar Zamfara a duk wani ƙoƙari na fannin rayuwar al’umma.
“Wannan ya nuna cewa ita mai goyon bayan APC ce kuma mai bin tafarkin dimokuraɗiyya da gaske.”
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Fatima Shinkafi a wannan aiki, kuma tana ɗaya daga cikin waɗanda suka kawo sauyi a fannin tattalin arziki da bunƙasa ma’adanai a ƙasar nan.