Salman Khan ya musanta samun saƙon barazanar da aka aika wa mahaifinsa

Daga AISHA ASAS

A jiya Alhamis jarumi Salman Khan ya bayyana wa jami’an tsaro cewar bai samu saƙon wasiƙar barazana ga rayuwarsa ba kamar yadda ake ta yayatawa. Ya kuma ƙara da cewa, bai samu wata hatsaniya ko saɓani da wani ba a wannan ɗan lokaci ba, duk da cewa kwana ɗaya kafin wannan furuci na jarumin, ‘yan sanda sun shigar da koken ƙarar wanda ba a san ko wane ne shi ba kan aika wa mahaifin jarumin, Salim Khan takardar da ake masa barazanar kisa a cikinta.

A wasu rahotannin sun tabbatar wasiƙar biyu ce, inda bayan ta mahaifin jarumin shima ya samu kwatankwacin ta, sai dai jarumin ya bayyana ko kusa bai samu makamanciyar abin da mutane ke faɗa ba, don haka ‘yan sanda suka amshi jawabinsa a rubuce don ci gaba da bincike kan lamarin.