Sama da ɗalibai 23,000 suka amfana da tallafin karatu na gwamnatin Jihar Nasarawa – Sa’adatu Yahya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Babbar Sakatariyar Hukumar Samar da Tallafin Karatu ta gwamnatin Jihar Nasarawa, wato Nasarawa State Scholarship Board a turance, Hajiya Sa’adatu Yahya ta ce kawo yanzu gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta bada tallafin karatu wa sama da ɗalibai ‘yan asalin jihar dubu 23 don ba su damar cigaba da karatunsu a manyan makarantun jihohin da ƙasa baki ɗaya.

Hajiya Sa’adatu Yahya ta sanar da haka ne a lokacin da take tattaunawa da wakilin mu a ofishin ta dake hukumar a garin Lafiya babban birnin jihar ranar Talata 1 ga watan Yulin shekarar 2023 da ake ciki.

Ta bayyana cewa daga cikin waɗannan ɗalibai ‘yan asalin jihar dama da dubu 23, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule ta kuma ɗauki nauyin tallafin karatun mutum 31 cikin su zuwa ƙasashen waje daban-daban don cigaba da karatunsu kawo yanzu.

Hajiya Sa’adatu Yahya ta ƙara da cewa har ila yau gwamnatin na Injiniya Abdullahi Sule ba ta fasa ba tana cigaba da ɗaukan nauyin karatun ɗaliban inda ta bayyana cewa a yanzu haka tuni gwamnatin ta hukumar samar da tallafin karatun ta fara shirye-shiryen sake fara tantance tare da sake sabon rabon tallafin karatun ga ɗaliban.

A cewar ta gwamnan wato Injinya Abdullahi Sule ya ga ya dace ne ya yi haka don agaza wa ɗalibai ‘yan asalin jihar dake karatu a manyan makarantu musamman don rage musu wahalhalu da ƙuncin rayuwa ke jawo da sauransu, inda a cewar ta kawo yanzu gwamnatin ta kashe sama da Naira miliyan 800 wa tallafin.

Ta kuma yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da wannan karamci da tallafin taimako na musamman da yake yi inda ta buƙaci ya cigaba da hakan.

A ƙarshe sai Hajiya Sa’adatu Yahya ta yi amfani da damar inda ta yi kira na musamman ga ɗalibai ‘yan asalin jihar ta Nasarawa bakiɗaya musamman waɗanda suka amfana da shirin kawo yanzu su tabbatar suna bai wa gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule cikakken goyon baya su kuma zauna lafiya a duk inda suke katarunsu don bai wa gwamnan damar cigaba da samar musu da ribobin dimokraɗiyya ta tallafin da sauransu don a ƙarshe kwalliya ta biya kuɗin sabulu.