Sama da maniyyatabn Kano 900 ne su ka rasa aikin hajjin bana

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sama da maniyyata 900, gami da jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ne za su rasa aikin Hajjin bana sakamakon matsalar rashin jirgin da zai yi jigilarsu.

Manhaja ta rawaito cewa tun da fari, Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bai wa kamfanin jirgin sama na Azman Air damar jigilar alhazan Kano, su 2,229 zuwa ƙasar Saudiyya.

Sai dai kuma Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta qi amincewa da jirgin Azman a bisa hujjar cewa ba shi da girman da zai kwashi alhazai da yawa a lokaci guda.

Wannan na zuwa ne bayan da a ka jibge alhazan, waɗanda suka fito daga ƙanan hukumomi daban-daban na jihar, a sansanin alhazai tun ranar Asabar ɗin da ta gabata ba tare da an kwashe su zuwa ƙasa mai tsarki ba.

Dama a ranar Laraba ne Saudiyya za ta rufe shiga ƙasar domin aikin Hajji, bayan ta ƙara kwana ɗaya a kan ranar da ta sanya za ta rufe bodojinta.

Babban sakataren hukumar, Muhammad Abba Ɗambatta, a wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, ya bayyana cewa ya miqa buƙatar canja jirgin da zai yi jigilar maniyyatan Kano daga Azman zuwa Max Air amma ta qi amincewa.

A cewarsa, ya zuwa ranar Litinin ɗin, mamiyyata 900 da wani abu kacal jirgin Azman ya kai Saudiyya a sawu 3, lamarin da ya sanya ya nemi agaji da ga NAHCON, wacce ta yi alƙawarin za ta turo jiragen Flynas guda biyu da na Azman guda ɗaya domin kwashe dukkan maniyyatan da kuma jami’an hukumar alhazai ta Kano.

A jiya Alhamis, rahotanni sun bayyana cewa jirgin Azman ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda ya kwashi alhazai 250 kacal, inda ya bar sama da 1,000 a qasa, har da Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano.

 Da yake zantawa da manema labarai a safiyar Alhamis, Ɗambatta, ya ce lamarin ya yi matuƙar sanya shi cikin halin damuwa, inda ya ɗora laifin a kan NAHCON saboda “gaza cika alƙawarin taimakawa wajen kwashe ragowar maniyyatan na Kano.”

Ɗambatta ya ce Alhamis jirgin AZMAN mai ɗaukar fasinjoji 400 zai tashi daga Kano ɗauke da maniyyata 250 kacal, inda ya bar sama da maniyata 940 tare da jami’an hukumar jin daɗin alhazai ta jihar.

Ɗambatta ya qara da cewa Azman Air ya kwashi maniyyata 1,175 a sawu shida sakamakon amfani da suke da qananan jiragen da ba su da girman ɗaukar maniyyata masu yawa.

Ya qara da cewa “wannan ne ya sa mu ka koka kafin a fara jigilar maniyatan aikin Hajji, ganin cewa muna da mafi yawan alhazai, kuma mun yi bayanin cewa mun fi son jirgin kamfanin Max Air ya ɗauki maniyyatan Kano saboda yawan maniyyatan da mu ke da su.”

 Sakataren  ya ƙara da cewa sau 11 ya na zuwa shelkwatar NAHCON da ke Abuja a kan wannan batu, ya ƙara da cewa ya rubutawa hukumar wasiƙu sama da 11 don kada a shiga cikin wannan hali, kuma shi ma gwamnan Kano da kansa sai da ya rubuta musu wasiƙa har sau 3 amma abin da aka koka akai sai da ya faru.