Sama da mutane 24,000 sun kamu da cutar mashaƙo a Nijeriya – NCDC

Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa an samu jimillar mutane 41,336 da ake zargin sun kamu da cutar mashaƙo a jihohi 36 da ƙananan hukumomi 350 daga shekarar 2022 zuwa mako na hudu na 2025. Daga cikin adadin, an tabbatar da 24,864 sun kamu da cutar, yayin da mutane 1,264 suka rasa rayukansu a jihohi 26 da ƙananan hukumomi 182.

Jihohin da suka fi fama da cutar sun haɗa da Kano (17,770), Bauchi (2,334), Yobe (2,380), Katsina (1,088), Borno (1,036), Jigawa (53), Plateau (31), da Kaduna (44). Hukumar ta ce jihohin nan sun ɗauki kashi 99.4 cikin ɗari na dukkanin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar. Bincike ya nuna cewa yara ne suka fi kamuwa da cutar, inda kashi 63.9 na waɗanda aka tabbatar sun kamu da ita ke tsakanin shekara ɗaya zuwa 14.

NCDC ta bayyana cewa allurar rigakafi na taka muhimmiyar rawa wajen hana yaɗuwar cutar, amma akwai giɓin rigakafi domin kashi 20 cikin 100 kawai na waɗanda suka kamu ne aka tabbatar da cewa sun karɓi cikakkiyar rigakafin cutar.

Hukumar ta buƙaci a ƙara ƙaimi wajen allurar rigakafi da kuma inganta hanyoyin sa-ido don daƙile yaɗuwar cutar cikin gaggawa.