Samar da ilimi da cigaban rayuwa: Yadda Abdulnaseer Bobboji ya taka rawar gani a Jalingo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Jalingo

A rayuwar duniya ta wannan lokaci, babu wani abu da a ke buƙatar ɗan Adam ya samu kamar ilimi na zamani da kuma na addini. Wannan ya sa ƙasashen da suka cigaba sika ɗauki ɓangaren ilimi da muhimancin gaske ta yadda su ke ba shi kyakyawar kulawar da ta dace, domin kuwa ana samun al’umma masu cigaba ta hanyar bunƙasar iliminsu ta kowanne ɓangare.

Domin masana sun ce babu wata al’umma da za ta ci gaba tana cikin duhun jahilci, don haka ne duk wata gwamnati walau ta tarayya ko ta ƙaramar hukuma da ta ke son cigaban jama’arta, to dole ne ta tashi tsaye wajen samar da hanyoyin da jama’arta za su samu ilimi domin su zama a sahun waɗanda suka cigaba.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Jalingo da ke jihar Taraba, Alhaji Abdulnaseer Bobboji yana  ɗaya daga cikin shugabannin da suka tashi tsaye, wajen nemar wa jama’arsu hanyoyin da za su samu ilimi da kuma gogewa a dukkan al’amuran rayuwa na yau da kullum.

Tun bayan zuwan sa shugabancin Ƙaramar Hukumar Jalingo a karo na farko ya samar da hanyoyin bunƙasa ilimi tun daga tushe da kuma yadda abin zai ɗore ba tare da samun tsaiko ba idan an samu tsawon lokaci. Wannan ya sa ko da ya dawo a karo na biyu sai da ya ƙara inganta hanyoyin da kuma faɗaɗa su.

Babbar hanyar da ya bi don samar da ingantaccen ilimi, shi ne yadda ya mayar da hankali wajen samar da kayan karatu a makarantun firamare da makarantun Islamiyya a ƙaramar hukumar, wannan ya sa duk wata makaranta walau ta boko ko ta Islamiyya da ta ke ƙaramar hukumarsa ta samu kayan aiki na koyarwa. Sannan su kansu ɗaliban sun samu kayan tallafi na littattafai da sauran su.

Baya ga haka, ya samar da tsarin horas da matasa a kan hanyoyin dogaro da kai wanda su ma matasa a wannan ɓangaren da damansu sun samu aikin yi domin su dogara da kansu, kuma ba an tsaya ga horas da su ba ne kawai ba, domin duk matasan da aka horas a duk wani fanni na sana’a to sai da aka raba musu kayan da za su je su riƙe kansu da shi a kan sana’ar da suka koya.

Ta ɓangaren matasa masu neman ci gaba kuwa a fannin karatun su, da dama sun samu rabon ɗaukar nauyinsu da ƙaramar hukumar ta yi a ƙarƙashin shugabancin Alhaji Abdulnaseer Bobboji, in da suka samu damar ci gaba da karatu a manyan makarantu na gaba da sakandare, don haka kullum matasa suke yabon sa tare da yi masa kirari da
‘Jagoran Cigaban Matasa.”

Duk da cewar Ƙaramar Hukumar Jalingo, ta yi fice a fagen ilimin boko tsawon shekaru masu yawa da suka gabata, amma ana ganin a wannan lokacin ta fi samun cigaba mai yawa  idan aka kwatanta da shekarun baya, wannan kuma kamar yadda jama’a suke faɗa ya samo asali ne daga tsayuwar daka da Alhaji Abdulnaseer Bobboji ya yi na ganin matasa sun samu kyakyawan tsarin ilimi wanda zai sa su zama sun riƙe kima da martabar da ƙaramar hukumar take da shi a shekaru masu zuwa.

Wani tsari da Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Abdulnaseer Bobboji ya samar da shi domin ƙara wa matasa ƙarfin gwiwar yin karatu shi ne, nuna musu da na gaba ake ganin zurfin ruwa, kuma magabata su ne abin koyi. Wannan ta sa aka shirya wani taro na musamman in da aka karrama manyan ‘yan boko ‘ yan asalin ƙaramar hukumar da suka yi fice a duniya, kuma suka bayar da gudummawar da za a ci gaba da amfanar ta tsawon shekaru masu zuwa.

A ƙarshen shekarar da ta gabata ta 2020, wato 31 ga watan Disamba an shirya wani babban taro in da aka karrama manyan masu ilimi da kuma masu tasowa na ƙaramar hukumar, wadanda suke da mataki na ƙololuwa wato farfesoshi da masu matakin dakta, da masu matakin kammala digiri na farko, wanda a taron an karrama mutane sama da 80 ‘yan asalin ƙaramar hukumar Jalingo. Cikin waɗanda aka karrama har da waɗanda Allah ya karɓi ransu, amma kuma har yanzu ana amfana da iliminsu a fannin cigaban rayuwa, cikinsu akwai Farfesa Abubakar Sa’ ad da Farfesa Ahmad Umar Jalingo  da Farfesa Musa Kalamullah Omar.

Sai kuma waɗanda suke da rai kuma suke ci gaba da bayar da gudummawar da su ma aka karrama su, kamar Farfesa Tukur Baba, Farfesa Abdulmumini Sa’ad, Farfesa Abbas Bashir, Farfesa Noku Michael, Farfesa Inuwa Muhammad da Farfesa Abubakar Jika.

A lokacin da yake jawabi a wajen taron, shugaban Ƙaramar Hukumar Jalingo, Alhaji Abdulnaseer Bobboji, ya yi kira ga matasa da waɗannan mutane da su zama abin koyi a gare su domin su ma su zamo abin alfahari a nan gaba, domin kuwa a cewarsa, “Mutum yana zama abin alfahari ne ta hanyar samun inganci a rayuwarsa, kuma Inganci ba zai samu ba sai da ilimi, don haka muke yin ƙoƙari don ganin jama’armu sun samu ilimi don su zama abin koyi, wanda kuma za su yi alfahari da abin da muka ɗora su a kai nan gaba.”

Daga ƙarshe ya ja hankalin matasa da su tsaya a kan hanyar neman ilimi domin samar da ci gaba a Ƙaramar Hukumar Jalingo da ma ƙasa baki ɗaya.
Shi ma da yake nasa jawabin a wajen taron, Galadiman Muri kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Tukur Abba Tukur, ya yi fatan kada taron ya tashi haka ba tare da an ɗauki darasin da ya ke cikinsa ba. Don haka yake cewa “mu za mu samar wa kanmu cigaba ba wani ba ne zai zo ya samar mana, kuma mu za mu samar wa kanmu zaman lafiya ba wani ba ne zai zo ya samar mana, don haka mu za mu taru domin mu samawa kanmu mafita, don haka mu ɗauki wannan taro da muhimanci, domin mu samar wa kan mu ci gaba mai ɗorewa.

Jama’a da dama da suka halarci wajen taron, sun nuna jin daɗinsu da yadda taron ya gudana kuma sun yi fatan alheri, da godiya ga Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Jalingo Alhaji Abdulnaseer Bobboji saboda hanyoyin da yake bi na samar wa ƙaramar hukumar cigaba.