Samun fetur a Arewa albarka ce, inji shugaban ’yan kasuwar manja a Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Tun bayan bikin ƙaddamar da samun man fetur na farko a tarihin Arewa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi kwanan nan a Komaila da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe, wasu wasu mutane suke ta cece-kucen cewa wai siyasa ce kawai don a zaɓi jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a 2023.

Sai dai kuma, shugaban ƙungiyar masu sana’ar cinikin manja na Jihar Gombe, Alhaji Usman Musa Chanji, ya ce sam batun ba haka ya ke ba, babu siyasa a ciki, mai makon haka ma, babban albarka ne wanda ’yan arewa ya kamata su yi alfahari da shi don ɗimbin alfanun da ke cikinta.

Alhaji Usman yayi wannan mamrtanin ne lokacin da ya ke nuna farin cika sa akan samun mai ɗin, yayin hira da wakilinmu a ofishin shi da ke babban kasuwa Gombe ranan Talatar da ta gabata.

A cewarsa, “ to idan mu ’yan Arewa ba mu yi murna da na’am da wannan albarkar ba, kuma bamu godewa shugaban ƙasa Baba Buhari ba, ai kenan munzama marasa godiyar Allah da wannan dama mai cike da tarihi da ta iso mu har gida, abun da a da sai dai mu riƙa dogaro da kudu, yau gashi mun samu, ai sai san barka, Alhamdulillah”.

Saboda haka, sai ya shawarci masu gunagunin akwai siyasa a ciki, su kawar da wannan da hasashe nasu, su gode Allah saboda inji shi yau in Allah ya yarda, batun rashin aikin yi a Arewa ko talauci ko rashin kuɗin shiga, sun kare, yana mai bada shawara ga al’ummar jihohin biyu, wato Bauchi da Gombe da su haɗa kawunansu, kuma su ba Gwamnati goyon baya don a sami nassarar kamala aikin tono mai ɗin har zuwa ƙarshe saboda cigaban yankin da ƙasa baki ɗaya.

Game da sana’ar manja a kuwa, shugaban ya koka saboda rashin tallafi ga mambobin ƙungiyar waɗanda ya ce harajoji sun addabi kasuwancinsu, yana mai nuni da cewa, rabonsu da morar wani tallafi tun zamanin mulkin tsohon gwamna Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo, kuma sun amfana matuƙa, saboda haka ina kuka ga mai girma gwamna, Muhammadu Inuwa Yahaya a madadin dubban yan ƙungiyarmu, da shima ya dube mu da idon rahama ya tallafa mana don mu ƙara bunƙasa sana’armu, da kuma baiwa matasa ƙarin ayyukan yi, baya ga bunƙasa tattalin arzikin jiha ta hanyar kuɗin shiga da haraji”.

Ya ce, a yau, daliln karyewar darajar Naira, kuɗin dakon manja da cinikin shi, sun yi tashin gwauron zabo saboda jigilar manja daga ƙasar Kamaru, ta biyo ta Ekan a jihar Ribas, kafin kuma ta iso Gombe, sai ɗan kasuwa ya yi kusan kasha duk ribar da zai samu bayan sayar da kayan shi.

Don haka, Alhaji Usman Musa Canji yake kira ga Gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen bunƙasa manja a cikin gida wanda zai ƙara taimakawa jama’a, su samu saye a cikin rahusa, har ila yau, kuɗin shiga ya ƙaru kuma manja ya yawaita, ba lalle sai an dogara da shigo da manja daga makwabtan ƙasashe ba.