
Daga BELLO A. BABAJI
Cibiyar kula da yaɗuwar cutuka a Nijeriya, NCDC, ta ruwaito cewa, mutane 1,319 ne suka rasa rayukansu a sakamakon cutar sanƙarau a Nijeriya.
NCDC ta bayyana hakan ne biyo bayan samun rahoton cibiyar aikin cutar sanƙarau ta gaggawa a Nijeriya (EOC) a shafinta na yanar gizo.
Cutar sanƙarau, wadda ake kira da ‘Diphtheria’ a Turanci, ta na shafar maƙogwaro ne hancin waɗanda suka kamu da ita wadda a sakamakon haka ake shan wahala wajen fitar da numfashi tsayawar bugun zuciya dai sauransu.
NCDC ta ce rahotanni 42,000 ne aka samu a shekarar 2022 a jihohin Nijeriya 37, inda ta bayyana ƙalubalen ake fuskanta wajen riga-kafi, rashin wadatattun ɗakunan aiki da jinkirin tabbatar da cutar.
Jihar Kano ta ɗauki kaso 75 na adadin waɗanda suka kamo da cutar, inda suka kai 18,108 cikin 25,812 da aka samu a ƙasar.
Sauran jihohin da suka samu kaso masu yawa sun haɗa da Bauchi_2,334, Yobe_2,408 da Katsina_1,501.
Haka kuma, cikin kesakesai 42,642, an tabbatar da guda 25,812, ko kuma kaso 60.5.
Sai wuraren da aka tabbatar a ƙananan hukumomi 184 na jihohi 26 da suka haɗa da; Kano_18,108, wadda ita ke da mafita yawan adadi; sai Bauchi_2,334; Yobe_2,408; Katsina_1,501; Borno_1,161; Jigawa_53; Filato_119; da kuma Kaduna_44. Waɗannan jihohi sun wakilci kaso 99.7% na adadin kesakesan da aka tabbatar na cutar.