Sanadin rubutu aka min tayin auren mata da gidan zama – Malam Muttaƙa A. Hassan

“Ina jin daɗin girmama ni da ake yi a matsayin marubuci”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Babu shakka kowa da baiwar da ubangiji Allah ya ba shi, ba tare da la’akari da girma ko shekaru ko arziƙi ba. A harkar rubutun adabi idan aka ambaci sunan Malam Muttaƙa A. Hassan daga Jihar Kano, marubucin littafin ɗaukar Jinka da wuya ka ji wata kalma da ba ta yabo ba na fitowa daga bakin mutane, har ma waɗanda ka ke tunanin ba abokan tafiyar sa ba ne. Ingancin halayensa, gogewarsa a wajen iya sarrafa labari, da kiyaye ƙa’idojin rubutu, ya sa har wani masoyinsa ya tava masa tayin ya auri ýar sa tare da alƙawarin zai ba su wajen zama, saboda yarda da nagartarsa, duk kuwa da kasancewarsa marubuci. Marubuta da dama na yi masa kallon bango majinginar manya da ƙanana, saboda sauqin kansa, haqurinsa, da son taimakawa ƙananan marubuta masu tasowa. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Malam Muttaƙa, da wasu ke yi wa laƙabi da Farfesa, ya bayyana sirrin samun nasararsa a gasar marubuta daban daban da shawarar yadda ƙananan marubuta za su samu ƙwarin gwiwa.

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka?

MALAM MUTTAƘA: Assalamu alaikum. Cikakken sunana dai Muttaƙa A. Hassan

Wanene Muttaƙa A. Hassan a taƙaice, me aka fi sanin ka a kai?

Asalin sunana na yanka shi ne Muhammad Muntaƙa, wataƙila kasancewata Bahaushe da ya taso a Ƙasar Hausa ya sa sunan rikiɗewa ake kirana a Hausance, wato; Muttaka maimakon Muntaƙa. Cikakken sunana shi ne Muttaƙa Abdullahi Hassan, amma a makaranta da kafafen sada zumunta an fi sanina da Muttaƙa A. Hassan. Haifaffen garin Kano ne, cikin Ƙaramar Hukumar Nassarawa, Unguwar Kawo.

Na fara karatun addinin Islama a makarantar allo da Islamiyya mai suna Ansarul Haƙƙ Islamiyya (safe da yamma) da kuma ta dare a Tahzeerul Aulad, duka a unguwar Kawo. Na yi firamare a Giginyu Special Primary School. Sannan na yi ƙaramar sakandire a Government Secondary School Tarauni, kafin daga bisani na tafi makarantar kwana (boarding) in da na kammala a sakandire ta haɗaka wato Government Unity Secondary School Ringim, Jihar Jigawa. Daga nan na dawo gida Kano inda na yi diploma a Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies inda na karanta Hausa/Islamic Studies/Education.

An fi sanina a sana’ata, ta P.O.P ceiling da rubutu; musamman rubutun da suka shafi sharhin wasannin ƙwallon qafa, sharhin littattafai, rubutun ayyanannen labari, siyasa da sauran dangogin rubutu na adabi.

Ba mu labarin yadda ka fara samun kanka a harkar rubutun adabi?

Dalilai ne da yawa. Amma duk wani dalili da zan hasaso a zuciyata ko na furta, yana bayan sha’awa, wato so. Son rubutu ne ya sa na ƙudiri niyyar fara rubutu. Kodayake ita kan ta soyayyar rubutun ta samu mafaka ne a zuciyata silar yawan karatu, wanda na fara tun ina firamare. Wataƙila wani ya yi tambayar ta ya ɗan firamare zai fara tunanin fara rubutu? Ba abin mamaki ba ne. Don na fara sha’awar rubutu tun ban iya karatu ba, karanta mana ake yi. Hasalima, idan zan faɗi abin da ya saka min nacin koyon rubutu sai in ce har da burina na son in ga ni ma ina rubuta labari. Hakan kuma ya samu asali ne tun da aka fara karanta mana littafin ‘Magana Jari Ce,’ da na ji tsuntsu na bayar da labari.

Amma ban fara rubutawa ba sai da na je qaramar Sakandire, inda na fara rubuta labaran yaƙi. Kafin daga bisani da na je makarantar kwana kasancewata marar saurin sabo, kaɗaici ya taimaka mani matuƙa wurin fara rubutun da ya shafi zamantakewa ta hanyar kamanta rayuwar da na tsinci kaina (ban san kowa ba) da rayuwa tare da abokaina na gida.

A lokacin na ware wani littafi da kullum idan tashi daga makaranta na dawo ɗaki sai na yi ta rubuta labari, a haka har wasu daga cikin ‘yan ɗakinmu suka lura ba na shiga mutane a yi wasa kullum sai rubutu. Ashe sun shirya ɗauke littafin ba tare da na sani ba, da suka ɗauke suka karanta sai kuma suka zo suna yaba mani. Sosai wannan ya ƙara min himma a rubutu.

Ka rubuta littattafai sun kai nawa, ba mu labarin wasu daga ciki a taƙaice?

Na rubuta littattafai aƙalla goma ko kusa da haka, sai kuma gajerun labaru waɗanda ba ni da lissafin adadinsu kasancewar nakan yi su lokaci zuwa lokaci.

Daga ciki akwai littafin ‘Babban Yaro’, wanda labari ne da ya shafi rayuwar irin mutanen da ba su da gashin wance, suke ƙoƙarin yin kitson wance. Ma’ana, irin waɗanda ba su da kuɗi, amma sukan takure kansu ta kowace irin hanya wurin ganin sun rayu a irin duniyar da masu hannu da shuni suke rayuwa, hakan kuma ya haifar musu da matsaloli iri-iri. Sai kuma labarin ‘Na Tsane Ki’.

Labarin wasu ƙawaye ne guda biyu (Amira da Amina) waɗanda suka shaƙu da juna matuƙa, babu wani abu da ke raba su ko da kuwa bacci ne. Har sai da ta kai ta kawo suna tsoron idan aurensu ya taso tilas za su rabu. Amma duk da wannan amincin, da mahaifin Amira ya ƙudiri niyyar auren Amina, tuni suka yi rabuwar kare da abokinsa, inda Amira ke taya mahaifiyarta kishi.

Akwai kuma littafin ‘Shahara’, wanda yake labarin wani shahararren marubuci ne, wanda wata buduruwa ta shigo rayuwarsa ta yi wasa da tunaninsa fiye da yadda yake wasa da alƙalaminsa yana sarrafa taurarin labarinsa, in da ta masa ƙofar rago ya nuna mata hanyar da za a iya bi a ƙwato wani ɗan ta’adda daga hannun jami’an tsaro.

Ta bi matakan ta ƙwato shi, shi kuma ya shiga ciki. Shin zai yi amfani da qwarewarsa a rubutu ne ya nemo ta tare da ɗanta’addan ko kuwa? Idan zai iya, ta ya yake iya kuvuta daga hannun jami’an tsaro? Sai idan an karanta labarin za a samu amsoshin nan. Na rubuta labarin ‘Ɗaukar Jinka, wanda shi an buga shi a matsayin littafi.

Labari ne da ya shafi ƙabilanci da sa-toka sa-katsin da ke faruwa tsakanin mabiya manyan addinai biyu na Nijeriya, wato musulmai da kiristoci. Me ya sa kan ƙabilun Nijeriya ba ya haɗuwa? Me ya sa duk da addinan biyu sun zo da zaman lafiya da dokoki amma mabiyansu ba sa ga maciji? Wacce matsala addinan ke hangowa a cikin Constitution ɗin ƙasa? Amsoshin na cikin littafin in shaa Allahu. Waɗannan dai su ne huɗu daga ciki.

Wacce gwagwarmaya ka sha a farkon fara rubutun wanne taimako ka samu, ko ƙalubale?

Gwagwarmaya kam ana kan yi. Da ke an yi batun farkon fara rubutu ne, zan ce ƙalubale ne gare ni, ba gwagwarmaya ba. Ƙalubale na farko kuma mafi muhimmanci shi ne, yadda lokuta da dama nakan ji a raina ina burin haɗuwa da wasu marubuta, amma ban san in da zan gan su ko na ce mu ga juna ba. Na sha ɗaukar lambar wasu marubuta a jikin littafansu, amma da ke lokacin akwai yarinta da kuma rashin sabo sai na yi ta tunanin idan na kira su me zan ce musu? Rashin sanin wannan amsar ya kan sa na kasa kira. Alhamdu lillah a yanzu akasarinsu ni da su mun san juna. Taimako kuma ba zai wuce shawarwari da na samu daga wasu manyan marubuta da kuma bita da na samu halarta.

Ka taɓa buga wani daga cikin littattafanka?

E, na buga ɗaya, ‘Ɗaukar Jinka’.

Wacce nasara za ka iya cewa ka samu a dalilin rubutu wanda ba za ka manta da shi ba?

Na sani, lokuta da dama idan an ce nasara, kai tsaye mutane sun fi tunanin cin gasa. Amma a wurina, ba wannan ce nasarar da ba na mantawa ba duk da kuwa na ci wasu gasanni. A tawa duniyar da na taso da burin haɗuwa da wasu marubuta, yau ya kasance ko a hanya suka gan ni za su gane ni har su kira sunana, wannan nasara ce.

Yadda na faro da rarrafe, har yanzu ta kai ta kawo wasu na kawo rubutun su na masu gyara ko na ba su shawarwari, nasara ce. Idan na tuna duk da har yanzu ni a wurina koyo nake yi a haka wasu na so na koya masu ɗan abin da na iya, wannan ma nasara ce.

Amma dai mafi girman nasarar da ba zan manta ba biyu ce: Na farko rubutu ya haɗa ni da manyan mutane waɗanda idan ba silar rubutun ba, wataƙila da ba za mu san juna ba, ta yiwu da ban amfana da karin maganar da ke cewa ‘Sabo da maza, jari ne’ ba. Na biyu mafi muhimmanci, silar rubutu na haɗu da wani bawan Allah da nake masa kallon uba, saboda silar rubuce-rubucena ya yi bincike a kaina da ya gama ya nemi lambata har ya zo da buƙatar zai mallaka mani ɗiyarsa tare da gidan da zan zauna.

Kodayake dai a lokacin ban karɓi wannan tayi ba saboda wani dalili nawa, amma har na bar duniya ba na manta wannan abu, har yanzu kuma akwai zumunci da mutuntawa sosai tsakanina da wannan bawan Allah. Saboda ƙarshen yarda da mutum zai yi da kai shi ne ya ba ka ɗiyarsa, don wanda ya ba ka ɗiyarsa musamman ma kyauta, ya gamsu ba za ka wulaƙanta masa ita ba ne. Har gobe idan na tuna rubuce-rubucena ne ke zuwa in da yake ba tare da ni na je ba, har ya yanke shawarar yi mani wannan abin arziƙi, nakan kasa manta alkhairin rubutu. Wani abu kuma, ko cikin fushi nake idan na fara rubutu nakan wuce har na yi wa murmushi shimfiɗa a fuska ta ya zauna.

Da dama an san ka ne a matsayin marubuci, me ya haɗa ka da hidimar siyasa kuma?

Da yake dai a rubuce ake ganin siyasar, kai tsaye sai na ce a nan ma rubutu ne ya haɗa ni da ita. Idan har marubuci zai iya ayyana labarin da bai faru ba ta hanyar nuni cikin nishaɗi don isar da wani saƙo da ke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya; sawa’un da niyyar a gyara, tsoratarwa, ilmantarwa; lallai a fagen siyasa ma yana da muhimmanci ya yi hakan.

Dalili? Saboda siyasa na da alaƙa da zaɓen shugabanni, su kuwa shugabanni kai tsaye suna da alaƙa da dukiyoyinmu, rayukanmu, da ma ƙimar mu. Don haka, yana da matuƙar kyau marubuci ya saka fitilarsa ya haska wa al’umma abubuwa da dama a cikin siyasa ta yadda mutane za su gane in da ya fi kamata su jefa ƙuri’ar su gudun kada su yi kitso da kwarkwata.

Menene ra’ayinka game da shigar marubuta da ýan fim cikin harkar siyasa?

Tana burge ni sosai. Duka ɓangarori biyun suna da rawar da za su taka wurin nuna wa al’umma nagarta ko raunin kowane shugaba, ta yadda mabiya za su gane wanda ya fi inganci cikin ‘yan takara. Sai dai, mafi takaici shi ne marubuci ko ɗan fim ya riqa tallata ‘yan siyasar da shi kansa ya san ba su da nagarta, wataƙila saboda an ba shi abin duniya ko saboda yana neman wani abu.

Lallai hakan yaudara ce kuma Allah ba zai ƙyale ba, na ji wani malami na fayyace duk wanda aka ba shi kuɗi ya tallata shugabannin da ba su da nagarta duk zaluncin da suka yi idan sun samu mulki yana da kamasho. Saboda haka, lallai yana da matuƙar muhimmanci shigarsu siyasa, sai dai yana da haɗari idan ba su yi tsakani da Allah ba.

Wanne cigaba ka ke ganin harkar rubutun adabi ta samu dangane da rubutun online?

An samu cigaba da dama kodayake wasu na ganin ya yi kama da na mai haƙar rijiya. Daga cikin cigaban da aka samu akwai:
Saurin Isar Da Saƙo: A yanzu marubuci ba ya buƙatar sai yana da kuɗin da zai buga littafi kafin ya isar da saƙo ga masu karatu, waya da data kawai yake buƙata ya aika saƙonsa in da yake so.

Samun Riba Da Kuɗi ƙalilan: Maimakon sai marubuci ya bi ta wasu hanyoyi masu tsayi na biyan kuɗin mai zanen bango, typesetting, printing har zuwa lokacin da zai zama littafi, da kuma rikici tsakaninsa da ‘yan kasuwa; a online data kawai yake buƙata (wataƙila sai kuɗin zanen bango) ya tallata rubutunsa kuɗi ya faɗo asusunsa kai tsaye ba tare da ka-ce-na-ce tsakaninsa da ‘yan kasuwa ba.

Kusanci Tsakanin Marubuta Da Makarantansu: Idan babu online, makaranci zai sha fama kafin ya iya haɗuwa da marubuci. Amma samuwar online, makaranci na kwance a lungunsu sai ya lalubo waya ya aika saƙo ga marubuci, sawa’un gyara, sharhi, tambaya ko ƙarin bayani.

Yaɗa Rubutun Hausa A Duniya: Ba na ko kokwanto idan na ce rubutu a online ya fi nisa fiye da a takarda. Dalili? A lokaci ɗaya marubuci na iya saka littafinsa a online wataqila yana Jigawa (sawa’un kafafen da ake sayarwa ko na kyauta) cikin ƙasa da awa ɗaya wani sai ya karanta a Kano, wani Kaduna, Niger, Abuja, Nasarawa, Kogi, ta yiwu ma ƙasashen ƙetare irin su; Nijar, Kamaru, Ghana da sauran in da masu fahimtar harshen Hausa suke. Idan ba a online ba, ta ya rubutun zai isa waɗannan garuruwa a cikin ƙanƙanin lokaci kamar wannan? Da kamar wuya, rayuwar kifi a doron ƙasa.

Kana ganin fitowar cibiyoyi irin su Gusau Institute cikin ƙoƙarin haɓɓaka adabi da bunƙasa harkar rubutun Hausa?

Kai tsaye sai na ce e, tabbas suna kawo ci gaba da ma bunƙasa adabi. Domin ita gasa kowace iri ce, tana saka marubuta su yi rubutu ko da ba su shirya ba. Har wa yau, tana saka marubuta su yi rubutu mai kyau, ko in ce su gyara rubutunsu. Za a gamsu da ni idan aka karanta duk wasu labaru da suka shiga gasar ko da kuwa ba su yi nasara ba, yawancin littafan za a iske suna ɗauke da salo na musamman, sababbin saƙo, tarin ilmi da sauransu.

Kana daga cikin marubutan da suka taɓa samun nasara a Gasar Rubutun Adabi ta Gusau Institute, menene sirrin samun nasarar ka?

Sirrin kawai shi ne sa wa da na yi a raina zan yi nasara. A ganina shi ne matakin nasara na farko, wato mutum ya yarda zai yi nasara. Daga nan kuma sai ya fara gina matakan nasara kamar: Na farko maimakon marubuci ya tsorata da cewa wane da wance suna cikin gasar, zai fi ya sa wa ransa lallai zai ƙalubalanci kansa ne ta hanyar ɗaura ɗamarar zuwa da sabon rubutu da ya zarce saura da ya tava yi, ta fuskar salo, zubi, jigo da saura.

Sannan yana da muhimmanci duk wani jigo da marubuci ya ɗauka, ya kalle shi ta wata fuska wadda sauran marubuta ba su kalla ba, wato ya tauna batutuwa a kai wanda malamai, mawaƙa da marubuta ba ta irin fuskar suka tauna ba, hakan zai mayar da rubutun sabo, bisa ɗabi’a ta ɗan Adamtaka kuwa duka muna ƙaunar sabon abu.

Abu na biyu, yana muhimmanci duk wata gasa da marubuci zai shiga, ya tattara littattfan da suka tava yin nasara a gasar ya karanta su, karatu na nazari; ina da yaƙinin hakan zai taimaka masa matuƙa wurin sanin ta in da ya fi dacewa ya tunkari gasar. Sai na uku, ya raka da addu’a.

Wani abu kuma muhimmi shi ne; idan duk da ya bi waɗannan matakai bai yi nasara ba, lallai kada ya sare, ya ci gaba da jarrabawa. Domin mai nasara ba ya sarewa, mai sarewa kuwa ba ya nasara. A sanina, babu wani mutum da yake nasara a kodayaushe a kan komai kamar yadda babu wanda yake faɗuwa kodayaushe a kan komai, lallai nasara da akasinta suna tare, wadda duk aka riska sai a sake jajircewa.

A lura da cewa a lokacin da yaro ke rarrafe, da zarar idanunsa sun nuna masa wasu na tafiya sai Allah ya kimsa masa tunanin shi ma idan ya jarraba zai iya tafiya kamar su. Amma da ya miƙe sai ya faɗi, gwanin burgewa faɗuwarsa ba ta hana shi sake tashi. Wannan nacin nasa kuma sai ya sa ƙafafuwansa su yi dakon gangar jikinsa har ya fara tafiya. Wannan kaɗai ya isa ya sa mu fahimci lallai nasara tana jin shakkar mutum mai naci.

Yaya ka ke ganin za a riƙa inganta irin waɗannan gasa?

Bayan mun karɓi sakamakon gasar Gusau Institute a shekarar 2022, an yi mana irin wannan tambayar sai na gaza bayar da amsa. Wataƙila saboda abin da na so cewa kamar zai ƙaro masu kashe kuɗi ne, kai tsaye kuma hakan ba daidai ba ne. Saboda kamar rashin gode wa ƙoƙarinsu ne, musamman yadda wasu cibiyoyi sun sha assasa gasa, amma da sun yi sau ɗaya sai su gaza sake yi.

Ke nan su da suka iya ci gaba da yi duk wata, lallai suna ƙoƙari. Bugu da ƙari, a da ba sa bayar da allon yabo (award) sai certificate, sannan ba a bayar da certificate ga waɗanda suka tsallaka zuwa zagaye na ƙarshe; amma a bara duka aka fara. Ko iya haka ma zan ce lallai an inganta. Duk da haka idan na hango wani gyara ko shawara in shaa Allah zan sanar masu.

Wanne tallafi da goyon baya ka ke ganin matasan marubuta na online ke buƙata a wajen manyan marubuta irin ku?

A matsayina na mai karambani ba a matsayin babba ba, ina bayar da lokacina don nuna goyon baya ga ‘yan uwana marubuta musamman masu tasowa ta hanyar nusar da su ɗan abin da Allah lamunce na koya. Ba rubutu kaɗai ba, Allah ya sani duk wani abu da na iya, na kan ji daɗi yayin da na koya wa wasu. Saboda kullum na kan amince ilimi wata kadara ce wadda da a ce rowarta ake yi, lallai da babu abu ɗaya da wani ya isa ya ƙware a kansa.

Wacce shawara ka ke da ita ga marubuta da ke son gwada basirar su a manyan gasanni marubuta da ake shiryawa?

Allah ya sani, babu wani marubuci ko marubuciya da ke kusa da ni da idan aka buɗe gasar rubutu ba na qarfafa masu gwiwa a kan su shiga. Idan kuma suka ɗaura ɗamarar shiga nakan ba su dukkan goyon bayana ko da ta hanyar ba su shawara ne ko gyara rubutun. A kullum nakan ce da su, “A shiga gasa babu faɗuwa sai nasara.

Domin aƙalla idan mutum ya shiga ko bai ci gasar ba yana amfanuwa da abubuwa aƙalla uku: Na farko ya yi nasarar samun ƙwarin gwiwar rubutawa (don wasu ba sa ma tsoron shigar suke yi) har kuma an karanta. Na biyu, zai gane dalilan da suka saka bai kai ga ci ba har ya gyara a wata gasar. Domin ban san wani abu da ke saurin gyara wa marubuta rubutunsu kamar gasa ba.

Menene burinka nan gaba a matsayin marubuci?

Ba don ba ya yiwuwa a raba rai da buri ba, da na ce ba ni da wani buri da ya rage mani a duniyar rubutu, wataƙila saboda ba ni da dogon buri a rubutu. In dai zan rubuta a karanta, lallai burina ya cika. Kodayake dai, akwai wani buri da nake son cim mawa, amma na bar wa zuciyata har zuwa lokacin da zan cika shi in shaa Allah.

Bangon littafin ‘Ɗaukar Jinka’

Wanne abu ne ya fi burge ka game da zamantakewar marubuta?

Marubuta mutanen kirki ne, wannan dalilin ne ma ya sa duk yadda marubuta suka man ba daidai ba, nake haƙuri saboda na san a matsayina na ajizi tilas na masu ba daidai ba sawa’un ina sane ko ba na sane, ta yiwu saboda kasantuwar su mutanen kirki ya sa ba sa mani ƙorafi. Babban abin burgewa a zamantakewar marubuta shi ne zumunci, girmama juna, taimakon juna tare da ƙaunar juna. Yana matuƙar burge ni yadda duk da wasu sun girme mani, wasu ma sun haife ni, yayin da wasu kuwa na girme musu, amma akan zauna a yi raha cike da girmama juna.

Menene ka ke ganin ya fi zama ƙalubale ga cigaban marubuta?

Ba don in da duk aka samu nasara tilas a samu kishiyarta ba, da na ce ban hango wani ƙalubale ba. Babban ƙalubalen da akasarin mu muke samu a cigaban rubutunmu, ba a basirar ƙirƙirar labari ba ne, yawanci a qarancin bincike ne. Abin da ake so ga cikakken marubuci shi ne, idan ya nuna tauraronsa likita ne, to mai karatu ya kalli likita a idonsa.

Idan ya nuna lauya ne, mai karatu ya hasaso wani ƙwararren lauya da ya san aikinsa. Idan ya nuna gwamna ne, lallai ne a samar da hoton zuci ga mai karatu ta yadda zai karɓi cewa lallai gwamnan ne. Hakan ba za ta taɓa samuwa ba sai an yi bincike a kan ayyukan waɗancan mutane an tabbatar ba a kuskure ba, sai kuma a zo a bi matakan ginin tauraro, ta hanyar la’akari da motsi, furuci, da sauran dabarun fayyace hoton zuci. Amma akasari marubuta ba ma son gyara, ga ƙiwar bincike.

Duk kuma rawar da wani tauraro zai taka, idan ya kasance an liqa masa aikin da ba a yi bincike ba, aka yi dace makarancin ya san wannan aiki da aka ba wa tauraron, lallai zai raina marubucin zai kuma watsar da rubutun ba tare da ya kai shi gaba ba.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ka?

Kowane tsuntsu, kukan gidan su yake yi. A duk lokacin da na nufi aikata wani abu marar kyau ita ce karin maganar da nake tunawa kuma take saurin dawo da ni saiti.

Sai kuma karin maganar da ake cewa, Hana Wani, Hana Kai. Sosai wannan karin maganar ma ke burge ni, saboda a sauƙaƙe ta fassara Hadisin da Annabi ya ce, “Imanin ɗayan ku ba zai cika ba har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa.” Kodayake da ma akasarin zantukan hikima ana samo su ne daga Ƙur’ani da Hadisi, saboda mafi hikimar zance shi ne zancen Allah, sannan na Annabinsa.

Na gode.

Madalla. Ni ma ina godiya.