Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Sanannen ɗan siyasa a Jihar Kano kuma shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta Jihar Kano Ambasada Ahmadu Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Ɗan Zago wanda gogaggen ɗan siyasa ne, ya kwashe shekaru da dama a harkar siyasa.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar REMASAB ne ya tabbatar da rasuwar Ahmadu Haruna Zago a asibiti.
A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban hukumar REMASAB.