Sanata Adamu ya naɗa Bala Ibrahim Daraktan Yaɗa Labarai na APC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya naɗa ɗan jarida a matsayin Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar.

Naɗin Malam Yusuf Bala Ibrahim a matsayin Daraktan Yaɗa Labarai na APC na ƙunshe ne cikin wasiƙar da babban ofishin APC na ƙasa ya fitar mai ɗauke da kwanan wata 1 ga Satumba, 2022 da kuma sa hannun Babban Mai Bai wa Shugaban APC Shawara kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Ambasada Samuel Jimba.

Wasiƙar ta nuna naɗin Ibrahim ya soma aiki ne nan take.

Yusuf Ibrahim ɗan asalin Jihar Kano ne, wanda ya yi karatu a gida da waje, inda ya soma aiki da BBC a 1988 a matsayin wakilin Kano, kana daga bisani ya taki matsayi daban-daban a BBCn.

Haka nan, ya taɓa riƙe muƙamin mai ba da shawara kan sha’anin yaɗa labarai ga tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Ibrahim Kpotun Idris; mai ba da shawara kan ayyuka na musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, da kuma mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai ga IGP
Usman Alkali Baba.

Kafin naɗin nasa, shi ne shugaban Hukumar Mujallar National Review.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *