Sanata Barau ya raba wa ‘yan fim ɗin Hausa motoci da babura a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, wato Sanata Barau I. Jibrin wanda aka fi sani da Maliya, ya yi taron bayar da tallafi ga ƙungiyoyin finafinan Hausa na Kannywood.

Taron wanda ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata a ɗakin taro na Mina Event Center da ke cikin birnin Kano, ƙarƙashin jagorancin Comrade Isayaku Abubakar Balan da kuma jami’in shirye-shirye Honarabul Nasiru Yusuf Shuwaki, wanda shi ne shugaban Kano Progressive Media Network (KAPMEN).

Tun da farko a jawabinsa, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar ya ce wannan tsari na Maigirma Sanata na tallafa wa ɓangarori na al’umma a rayuwar su ba ƙaramin abu ba ne a jihar Kano kuma shi ake  buƙata. 

Ya ƙara da cewa, “na zo wajen taron nan ne saboda na gamsu cewa a nan gaskiya take, kuma Sanata Barau al’umma ne a zuciyarsa.

“Ina kira gare ku da ku dage wajen shirya finafinai masu inganci na addini da al’adunmu, domin toshe duk wata kafa ta koke-koke daga mutanen mu, babban burin mu a matsayinmu na iyayenku shi ne, wannan sana’a taku ta bunƙasa ta hau matsayi babba a duniya,” inji Farfesa Hafizu Abubakar.

Da ya ke wakiltar ɗimbin jaruman da suka halarta, Jarumi Ali Nuhu ya ce da yawa daga cikin ‘yan Kannywood dama ‘yan jam’iyyar APC ne tun a 2015, don haka tafiyar Sanata Barau Maliya ba yanzu suka fara ba, kuma ƙuri’arsu ta zaɓen gwamna 2023 a Kano ta sa ce.

Ali Nuhu ya gode wa Sanata da irin wannan kaɓakin alheri da ya baiwa ‘ya’yan wannan masanarta ta Kannywood wanda zuwa yanzu babu wanda ya tava yi sai Maliya.

An dai raba wa jaruman Kannywood da mawaƙa motoci guda 17, babura guda 100, sai na’urar kwamfuta guda 80.

Daga cikin waɗanda suka rabauta da motoci sun haɗa da Ali Nuhu, Adam A. Zango, Hajara Usman, Yakubu Muhammad da Fati Muhammad.Sauran su ne
Ɗan-ƙuda, Baba Ari, Ado Gwanja, Falalu A. Ɗorayi da sauransu.

Taron dai ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau, Hon. Amadu Haruna Zago, Hon. Murtala Alasan Zainawa da Hon. Shitu Madaki Kunchi da Hon. Yusuf Tumfafi da Hon. Abdullahi Magaji Lamba Bichi da Hon. Ɗan Sharu Bebeji da Hon. Isyaku Abubakar.

Daga ƙarshe dai masu  barkwancin nan (Baba Ari) da su Daushe sun gabatar da taƙaitaccen wasan kwaikwayo a wurin. taron dai ya samu halartar jarumai maza da mata da ke masana’antar finafinai ta  Kannywood.