Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa.

Kwamshinan Zaɓe na Jihar Adamwa, Farfesa Hudu Yunus Ari, shi ne ya bayyana nasarar Binani wadda ta kasance ‘yar takarar Jam’iyyar APC.

Da fari, Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP ne ke gaba da yawan ƙuri’u kafin daga bisani Binani ta shige gabansa.

Magoya bayan jam’iyyar PDP sun nuna rashin jin daɗinsu ganin Kwamishinan Zaɓe na jihar ne ya bayyana sakamakon zaɓen maimakon Baturen Zaɓe.

Da wannan nasarar da ta samu, a iya cewa Sanata Aisha ta zamo mace ta farko da ta taki matsayin gwamnan a tarihin Nijeriya.