Sanata Lawan ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga WAKILINMU

Shugaban Majalisar Dattawa kuma ɗan takarar sanata na APC a Yobe ta Arewa, Ahmed Ibrahim Lawan, ya kaɗa ƙuri’arsa cikin nasara.

Ya kaɗa ƙuri’ar tasa ce a rumfar zaɓen da ke makarantar firamaren Katuzu da ke Gashua, Ƙaramar Hukumar Bade, Jihar Yobe.

Lawan ya kaɗa ƙur’ar ne da misalin ƙarfe 11:01 na safe, inda ya yaba wa hukumar zaɓe INEC dangane da ƙoƙarin da ta yi wajen shirya wannan zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *