Sanata Lawan ya lashe mazaɓarsa a Yobe ta Arewa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya lashe mazaɓarsa ta Arewacin Yobe da gagarumar nasara a zaɓen majalisun tarayya da na Shugaban ƙasa wanda ya gudana ranar Asabar a faɗin kasar.

Da take sanar da sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Lahadi, Baturiyar zaɓen (Returning Officer), Farfesa Omolola Aduloju, daga Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashu’a, a cibiyar tattarawa da sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi shida na Yobe ta Arewa, Bade, Jakusko, Karasuwa, Nguru, Yusufari da Machina, ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen.

Ta ce a cikin adadin ƙuri’un da aka yi rijista a ƙananan hukumomin, kimanin 122136, da yawan ƙuri’un da aka jefa a zaɓen 126677, sannan kuma da ƙuri’u 4541 da suka lalace; jam’iyyar NNPP ta samu ƙuri’u 7210, sai PDP mai kuri’u 22849, yayin da jam’iyyar APC ta samu adadin ƙuri’u 91318 a ilahirin ƙananan hukumomi shida a yankin.

Jami’ar zaɓen ta bayyana cewa, “Ni Farfesa Omolola, a matsayin Baturiyar zaɓe a Yobe ta Arewa, wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, zaɓe ne da yan takara suka fafata. Kuma bisa dokar hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Sanata Ahmed Lawan na jam’iyyar APC shi ne ɗan takarar da ya zarta abokan takararsa da yawan ƙuri’u 91318, saboda haka na ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaɓe a Yobe ta Arewa.”

Kamar yadda sakamakon ya nuna, Sanata Lawan ya doke abokan takararsa na jam’iyyar PDP, Hon. Ilu Bello Yusufari, wanda ya samu ƙuri’u 22849, da kuma Hon. Daiyabu Garba Hamza na jam’iyyar NNPP mai ƙuri’u 7210, da Hon. Sheriff Alhaji Bunu na jam’iyyar ADC mai ƙuri’u 756.

Bugu da ƙari, an gudanar da zaɓen tare da sanar da sakamakon zaɓen a gaban wakilan yan takara da na jam’iyyu, jami’an tsaro da yan jaridu tare da masu sanya ido, cikin tsanaki da kwanciyar hankali.