Sanata Lawan ya tallafa wa al’ummar mazaɓarsa da shinkafa da gero

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa, Dr. Ahmad Lawan, ya tallafa wa al’ummar mazaɓarsa da kayan abinci kimanin buhuna 9000 na hatsi da shinkafa don rage raɗaɗin tsadar rayuwa a yankin.

Wannan matakin tallafin na Sanata Lawan, daɗi ne a kan makamancin sa wanda Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Yobe suka ɗauka wajen rage wa al’umma wahalhalun da suke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.

Sanata Ahmad ya ƙaddamar da tallafin kayan abincin, wanda Gidauniyar ‘SAIL’ ta ɗauki nauyin aiwatar da shi a cikin gundumomi 60 da ke Yobe ta Arewa.

Taron raba tallafin ya gudana ne a ranar Asabar a Filin Ƙwallon Ƙafa dake unguwar Katuzu a garin Gashuwa ta ƙaramar hukumar Bade a jihar Yobe.

Tallafin ya ƙunshi buhun shinkafa 6000 da na gero 3000.

An raba tallafin ga ƙungiyoyin addinai da nakasassu da masu ƙaramin ƙarfi daga yankunan ƙananan hukumomi shida na Yobe ta Arewa: Bade, Nguru, Jakusko, Karasuwa, Yusufari da kuma Machina.

Haka zalika, Sanata Lawan ya hannunta sabuwar makarantar sakandire, ‘Federal Science and Technical College, Gashu’a’, wadda Gwamnatin Tarayya ta gina a mazaɓarsa ga Gwamnatin Jihar Yobe domin miƙa ta ga Gwamnatin Tarayya a hukumance ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

Sanata Lawan ya bayyana cewa, “Muna sane dangane da halin da al’ummarmu suke ciki na tsadar rayuwa, wanda bisa ga wannan mu ka ga ya zama wajibi mu tallafa wa jama’a don rage wahalhalun da ake fuskanta.”

A hannu guda kuma, wasu ɓata-garin matasa sun daka wawa a kason kayan abincin da aka ware domin al’ummar unguwannin Sabon Gari da Sarkin Hausawa dake cikin garin na Gashuwa, kimanin buhunan shinkafa 200 da gero buhu 80.