Sanata mai wakiltar mazaɓar Buhari ya fice daga APC zuwa PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanatan dake wakiltar shiyyar Daura, mahaifar Shuagaban Nijeriya Muhammadu Buhari, wato Sanata Ahmad Babba Kaita, ya fice daga jam’iyyarsa ta APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Babba-Kaita ya canja sheƙa zuwa PDP ne ranar Laraba, saboda rashin jituwa da suke samu tsakanin sa da gwamnan jihar Aminu Masari.

A wasiƙar da ya aika wa Manhaja, mai magana da yawun sanatan, Malam Abdulƙadir Lawal, ya ce Sanata Babba Kaita ba ɗan amshin shata ba ne.

”Ni ba irin ‘yan siyasan nan ba ne da ake yi wa laƙabi da ‘yan amshin shata. Ba zan amince da hakan ba, kuma hakan shine dalilin da ya sa na tattara kaya na na fice daga APC.

”Jam’iyyar PDP ce jam’iyyar da ta dace da ni ba APC ba. Saboda haka na haƙura da APC na koma gidan da ya fi dacewa da ni a siyasance.”

Sanata Babba Kaita ba su ga maciji da Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari wanda ya ke zargi da yin babakere a jam’iyyar APC a Katsina ba tare da ya bai wa sauran ‘yan jam’iyyar dama su taka rawar su a ba domin cigaban jam’iyyar.