Sanata ya ɗauki nauyin koyar da matasa da mata sama da 1000 sana’o’i a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar mazaɓar Kebbi ta Arewa da kuma Hukumar Yawon Buɗe Ido (National Institute for Hospitality and Tourism da kuma Muhasaf Global Resources Ltd ) ya ɗauki nauyin koyar da matasa da mata sama da dubu ɗaya sana’o’in hannu a faɗin mazaɓarsa.

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da koyon sana’o’in Alhaji Sama’ila Ɗantagago a madadin Sanata Yahaya Abubakar ya bayyana cewa koyon sana’o’i ya zama wajibi ga kowane mutum don kare mutuncinsa da na iyalansa, da zarar mutum ba ya da sana’a ba shakka zai zama taulali a cikin al’umma wanda ƙasƙanci ya kan biyo baya.

Ya kuma ja hankalin matasa da himmatu wajen neman abin yi saboda rage dogara ga gwamnati musamman a irin wannan yanayin da aikin ke da wahala.

Haka zalika ya ƙara nanata cewa Sanata Yahaya zai cigaba da bayar da wakilci kamar yadda ya saba wanda shi ne ya ba sanya matasa suka jajirce suka tsaya kai da fata suka ba shi goyon baya har ya sake komawa majalisar dattawa har karo na uku wanda ba shakka yanzu su ne ke bin sa bashi saboda haka su cigaba da ba shi goyon baya kuma su guji bangar siyasa su zama jakadu nagari a duk inda suka samu kawunansu.

Ya ƙara da cewa kamar yadda ku ka sani wannan mazaɓar ta gundumar mazaɓar Kebbi ta Arewa tana da ƙananan hukumomi 6 da suka haɗa da Argungu, Augie, Arewa, Dandi, Suru da kuma Bagudo za a gudanar da irin wannan a kowace ƙaramar hukuma saboda sauƙaƙawa kowa wajen tafiya mai tsawo bisa ga la’akari da yanayin da ake ciki.

Ya yi kira ga matasan da suka ci moriyar wannan shirin da su dage su yi amfani da ilmin da suka samu kada su yi watsi da shi. Haka zalika waɗanda ba su samu shiga ba a wannan karon su yi haƙuri ba da daxewa ba akwai shirye-shirye da ke tafe ba da daɗewa ba su ma in Sha Allahu za su samu shiga.

Kuma bayan kammala wannan zaman za a bai wa kowa wani abu da zai iya fara sana’a da shi.

Abdullahi Magaji Always ɗaya daga cikin waɗanda suka samu shiga cikin wannan shirin ya yaba wa Sanata Yahaya Abubakar bisa ga kulawar da ya ke bai wa matasa musamman wajen samar da sana’o’i, idan kowane ɗan siyasa zai yi haka in Sha Allahu kafin ƙarshen shekaru 4 za a rage zaman banza tsakanin al’umma.

Ya yi kira ga ‘yan siyasa da su yi koyi da shi wajen aiwatar da irin waɗannan shirye-shirye da kuma aiwatar da ayyukan cigaban al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *